“Waƙa adabi ce, shi kuma adabi al’ada ne”
Daga IBRAHIM MUHAMMAD
(Danmadamin Birnin Magaji)
0.0 Shimfiɗa
Hausawa musamman mazauna karkara (ƙauyuka) suna wanzar da al’adu da yawa masu sha’awa da adana tarihin wannan al’umma. Waɗannan al’adun su ne taskokin da suka adana tarihinmu. Kuma waɗannan al’adu su ne suka samar da adabimmu. Wajen wanzar da al’adun aure ake samar da waƙoƙin aure. Wajen wanzar da wasanni ake gwada yin salailan maganganun hikima da gwada zalaƙar harshe. A nan salon magana da adon magana da karin magana ke tasowa. A nazarin tarihi da rayuwar wannan bawan Allah an ci karo da al’adun Hausawa masu tarin yawa waɗanda za a ga tasirinsu a cikin tattaunawar wannan maƙala.
An nemi a gabatar da asalin Makaɗa Muhammadu Bawa ɗan’anace ta ɓangaren mahaifinsa da kuma tarihin sauya mazaunin mahaifansa zuwa inda aka haifi Muhammadu Bawa ɗan’anace wato ‘Yartsakkuwa, wadda ke yankin Gandi, ƙaramar Hukumar Mulki ta Raba a Jihar Sakkwato. Mazauna wannan yanki haɗaka ne, domin ƙabilu ne mabambanta suka haɗa mazauna ɗaya kamar Fulani da Hausawa da Gobirawa da Zamfarawa suna hulɗayya daban-daban tsawon lokaci.
Akwai tarihin shiga sabgar waƙa inda aka zo da bayanin yadda ɗan’anace ya fara waƙa, waƙarsa ta farko kan wani fanni da ba na dambe ba, da kuma waƙarsa ta farko ta dambe. An nemi sunanyen wasu daga cikin waɗanda ya yi ma waƙoƙi, da kuma waɗanda yake yi ma waƙa har zuwa shahararsa da kuma wafatinsa. Wannan ɓangare shi ne ya haska wa masu nazarin waƙar baka, iri gudummuwar da wannan makaɗi ya bayar ga adabin baka na Hausa.
Waƙoƙin Muhammadu Bawa ɗan’anace kundin tarihi ne. Abubuwan da za a tsinta a ciki suna da yawa. Kaɗan daga cikinsu za a ambata a nan, saura kuma za a gansu a ƙumshiyar maƙalun da za a gabatar a wajen wannan taro in sha Allahu. Waƙa adabi ce, shi kuma adabi al’ada ne. Saboda haka waƙoƙin baka suna adana al’adun Hausawa domin kusan kowane fanni na rayuwar Bahaushe zaka tarar da waƙoƙi sun wanzu a cikin wannan fanni. Misali, idan aka ɗauki waƙoƙin gargajiya da ake wanzarwa a lokuttan bukukuwan al’ada kamar a lokuttan da ake yi wa yara kaciya, idan za a yi bukin fita kaciya (mako biyu ko uku) makaɗa kan ƙawata wannan buki da kaɗe-kaɗe da waƙe-waƙe. A nan kam al’adu sun cakuɗu da adabi, har in ba a tantance ba, sai a rasa gane shin waƙoƙi al’adu ne ko adabin baka. A lokacin da wanzamai ke zagayen yin tsaga irin na al’ada a ƙauyuka da tungai-gai tare da makaɗa da mawaƙa ake gabatar da wannan shagali. Haka nan wasannin dambe da kaukawa da wasannin tauri da farauta, dole sai da kiɗi da waƙa.
Da wannan ‘yar gajeruwar shimfiɗa, ake son a bayyana cewa shi wannan makaɗi ya raya al’adun dambe, ya raya na sana’ar noma, ya raya na waƙoƙi, wanda sanadin hakan rayuwarsa ta adana tarihi ba na kansa da iyalansa kaɗai ba, har ma da na al’ummarsa ta Hausawa. Bayanan da za su biyo baya, za su kawo hoton yadda ya yi rayuwa da kuma su wane ne abokanin hulɗayyarsa.
Tushen Alhaji Muhammadu Bawa ɗan’anace ‘Yartsakkuwa, Gandi Sakkwato:
Kagarar Rima da ke cikin ƙasar Gwaranyo ta yanzu misalin kilomita sittin (60) daga garin Sakkwato a nan ne Allah ya tayar da wasu iyalai da suka haifi Baƙo mai Jirgi. Sunan Baƙo na yanka shi ne Abdullahi, Sunan mahaifinsa Muhammadu sunan kakansa wanda ya haifi mahaifinsa Abubakar sunan ƙanen mahaifinsa Ummaru. Sana’ar Sarkanci ita ce suka gada kaka da kakkanni. Kuma ita suke yi har wafatinsu. Yanzu haka Malam Musa Shu’aibu Sarkawa shi ne Sarkin Sarkawan Kagarar-Rima shi ke riƙe da wannan sarauta. Malam Musa ya gadi wannan sarauta daga mahaifinsa Shu’aibu. Kafin a kawo ga Malam Musa Shu’aibu, Kakanni da Iyayen Baƙo mai jirgi su ne suka riƙe wannan sarauta tsawon lokaci. Domin Abubakar Kakan Baƙo ya yi Sarkin Sarkawan Kagarar-Rima kafin rasuwarsa. Kakakkani da iyayyen Baƙo sun riƙe wannan sarauta, kafin wannan sarauta ta koma gidansu Malam Shu’aibu.
Daɗaɗɗiyar al’ada ce ga mutanen wannan yanki na Kagarar-Rima da kuma yankin da Hausawammu suke zaune, a aika yaro tun yana ƙarami ko matashi wajen mahaifarsa domin ya koyi wata sana’a ko ya samu wani ilmi wanda ba a yi a mahaifarsa. Har yanzu akwai wannan al’ada a ƙasar Hausa.
An tura Baƙo a ƙauyen ‘Yartsakkuwa domin neman ilimi irin na addinin musulunci a wajen Malam Liman ɗanbabba na ‘Yartsakkuwa. Baƙo na daga cikin almajiran da ke ɗaukar karatun addini a wannan makarantar. ɗalibi a yawon neman abinci irin wanda almajirai ke yi in sun samu sukuni daga makarantar allo, Allah ya jefa shi gidan Sarkin Makaɗan ‘Yartsakkuwa Alasan.
A nan Baƙo yake zuwa yana yi musu hidimar gida, kuma iyalan Sarkin kiɗa Alasan su ne suka nemi ya zame musu yaron gida mai yi musu hidmar gida (aikace-aikacen tsakar gida da na aike zuwa waje) nazartar tarbiyarsa ce suka ga su kam sun samu yaro mai haƙuri da tarbiyya. A kwana a tashi, baƙo ya zama ɗan gida. Masu gidan suka sha alwashin riƙe shi har koda yaushe in dai yana da ra’ayin ya ci gaba da zama da su bisa ladabi da biyayya. Kwanci tashi shekaru suka raka har Sarkin Makaɗa Alasan ya aurar da Baƙo daga ciki gidansa wanda aka yanka masa kewaye a cikin gidan Sarkin Makaɗa, Allah ya yi zamansa a gidan har wafatinsa. Bayanai kan zuri’ar Baƙo suna nan tafe a cikin wannan tsakure in sha Allahu.
Baƙo yana ‘Yartsakkuwa a gidan Sarkin kiɗan Sansanin’Yartsakkuwa Malam Alasan na ‘Yartsakkuwa Malam Alasan, ɗan’uwansa Isah Mai Jirgi suna a can Sabon Birnin Banaga, ta masarautar Anka, Jihar Zamfara a halin yanzu. Isah Mai Jirgi sunan mahaifinsa Abdullahi, shi kuma Baƙo Mai Jirgi sunan mahaifinsa Muhammadu. Da Abdullahi da Muhammadu duka ɗiyan Malam Abdullahi Mai Jirgi ne, Sarkin Sarkawan Kagarar Rima. Sana’ar waɗannan mutane ita ce sarkanci wato sassaƙa jirgi na ice ko kwale-kwale na katako domin a yi fito a cikin ruwa da kuma kamun kifi.
Mahaifan Muhammadu Bawa ɗan’anace ‘Yartsakkuwa
Abdullahi (Baƙo) Mai Jirgi ɗa ga Muhammadu Mai Jirgi, jika ga Abdullahi Mai Jirgi Sarkin Sarkawan Kagarar Rima, Gwaranyo Jihar Sakkwato (1882 -1936) shi ne mahaifin Muhammadu Bawa ɗan’anace. Waɗanda aka tattauna da su domin nemn sahihan bayanai kuma ‘yan uwa na jini ga Baƙo Mai Jirgi ba su bada shekarar da aka haife shi ba. Sun dai ce yana da kimamnin shekaru goma (10) na haihuwa ya bar gida zuwa ‘Yartsakkuwa. Ammai dai sun shaidarda laƙabinsa na Mai Jirgi ya samo asali ne saboda sana’ar da suka gada kaka da kakkanni, kuma har ya bar gida wannan sana’ar ita yake yi kafin ya koma ‘Yartsakuwa da zama domin neman ilmi irin na muhammadiyya. Malama Majiya ta ankarar da masu wannan bincike cewa, su suna koya wa yaransu sassaƙar jirage ko kwale-kwale tun suna yara ƙwarai da gaske. Koda za a yi wa yaro Kaciya, to lallai ya iya sassaƙa jirgi wanda ana iya kai shi kasuwa a sayar ko bakin ruwa a yi hitoo da jirgin.
Ta fuskar asali na mahaifi, mutanen Kagarar Rima da ke Gwaranyo, Gobirawa ne waɗanda suka samu mazauni a nan Kagarar Rima har suka gidandanje. Baƙo Mai Jirgi mahaifin Muhammadu Bawa, Bagobiri ne na asali. Mahaifiyarsa kuma Bazamfara ce.
Wace ce Mahaifiyar Muhammad Bawa ɗan’anace?
‘Yar Abu magajiyar Anace ita ce mahafiyarsa.
Mene ne Sunan ‘Yar’abu na yanka?
Aminatu shi ne sunanta na yanka.
Wane ne Anace?
Anace shi ne ƙanen ‘Yar’abu. Su uku ne kacal mahaifinsu ya haifa. Anace, ‘Yarabu sai Jibo Mahaifinsu kuma shi ne Malam Alasan Sarkin Makaɗan ‘Yartsakkuwa. Ga asali na iyaye Anace da ‘Yar’abu Zamfarawa ne saboda Malam Alasan Mahaifinsu Bazamfare ne. Uba Bagobiri, uwa Bazamfara su ne suka haifi Muhammadu Bawa.
Mahaifar Muhammadu Bawa ɗan’anace ‘Yartsakkuwa:
Malam Alasan ya sha alwashin zai haɗa zuri’a da Baƙo mai jirgi saboda ya yaba da tarbiyarsa a lokacin da yake barance a gidansa a ‘Yartsakkuwa. Baƙo mai jirgi ya isa ‘Yartsakkuwa domin samun karatun allo yana da shekaru goma kacal da haihuwa. An bashi auren ‘Yar’abu yana da shekaru shatakwas (18) a duniya. Ya haifi ɗansa na farko Muhammadu Bawa yana da shekaru Ashirin a duniya, ita kuma ‘Yar’abu a lokacin tana da shekaru sha-shidda (16) da haihuwa. Shi kuma Anace yana kimanin shekaru Ashirin (20) a lokacin da ‘yar uwarsa ‘Yar’abu ta haifi ɗanta na farko Muhammadu Bawa.
Anace shi ne ya gaji Malam Alasan da sana’ar kiɗi. Shi kuma Muhammadu Bawa ya gaji Anace (Kawunsa, ƙanen mahaifiyarsa) da sana’ar kiɗi. muhammadu Bawa ya samo laƙabinsa na ɗan’anace, ga kawunsa. Anace ya yi sarautar Sarkin kiɗi tun kafin mahaifinsa ya rasu. Shi kuma ɗan’anace ya ɗora daga inda Anace ya bari har zuwa wafatinsa. ɗan’anace ya zama Karen makaɗa kenan, domin Mahaifinsa bai yi kiɗa ba, amma kakansa da kawunsa sun yi.
Shekarun Alhaji Muhammadu Bawa ‘Yartsakkuwa:
Yanada kyau a san ra’ayoyin malamai kan shekarun Muhammadu Bawa ɗan’anace ‘Yartsakkuwa. Irin waɗannan bayin Allah shekarunsu kan shige duhu saboda a zamanin da aka haife su, da wuya in an je asibiti a lokacin haihuwarsu. Kuma ko an je asibitin mai yiwuwa ba a karɓi wata shaidar haihuwarsu ba, da za ta gwada shekara da kwanan watan haihuwar. Wannan yanayi na rashin sanin haƙiƙanin sadda aka haifi mutum, yana faruwa ga mutane da yawa ba ma ga makaɗa kaɗai ba. Gusau, S. (1996) ya ruwaito ce an haifi ɗan’anace a shekarar 1914-1986. A sharin da Gusau ya gabatar kan makaɗa ɗan’anace, an ga cewa, shaihin malamin ya taɓa haɗuwa har suka tattauna da shi ɗan’anace a wasu lokutta. ɗan’anace ya rayu shekaru saba’in da biyu (72), a bisa bayanin da ke cikin littafin Makaɗa da Mawaƙan Hausa.
Yahaya ɗan’anace, wanda ɗa ne ga ɗan’anace amma ba na cikinsa ba. Anace shi ne mahaifin Bawa Na-Alai. Shi kuma Bawa Na-Alai shi ne mahaifin Yahaya ɗan’anace. Da Bawa Na-Alai da Muhammadu Bawa ɗan’anace, taubasan juna ne, saboda iyayensu ‘ya’ya ne ga Makaɗa Alasan. Makaɗa Alasan kenan ya haifi ‘ya’ya ukku ne a rayuwarsa (Aminatu, Anace da Jibo). Da wannan shimfiɗar ake son a ce, shi Yahaya, ɗa ne ga ɗan’anace, jika ne ga Anace. To Yahaya ya yi yawon kiɗa wato bara ga ubansa ɗan’anace. Kamar yadda shi ma ɗan’anace ya yi zama baran kawunsa Anace. Shi Yahaya ɗan’anace mai shekaru sittin (60), ya tashi ƙarƙashin ɗan’anace tun daga yaye (yana ƙasa ga shekaru goma 10). Ya shaidarda cewa, ya ziyarci wurare da dama tare ɗan’anace wajen yawon kiɗa.
Yahaya ɗan’anace ya bayyana wa mai wannan bincike cewar ya sha zaman tattaunawa da ɗan’anace domin sanin tarihin kiɗa a matsayinsa na mai koyon sana’a a wajen ɗan’anace. A cewar Yahaya koda aka haife shi a shekarar 1966, shi ɗan’anace yana da shekara sittin da biyar (65) kuma ya yi shekaru Hamsin da biyar (55) a cikin sana’ar waƙa. A wannan tawili, Yahaya yana bayyana cewar ɗan’anace ya fi shekaru saba’in da biyu (72) a tsawon zamaninsa a duniya. A fahimtar wannan tsakure ta bayanin ɗan’anace a bakin Yahaya Anace, ɗan’anace an haife shi a shekarar 1901 ya rasu 1986, kenan ɗan’anace, ya yi shekara tamanin da biyar (85) a duniya.
ɗan’anace ya yi wafati a shekarar 1986 a ‘Yartsakkuwa, ya bar matan aure ukku (3) Hajiya ‘Yar-Magishiri da Hajiya Rabi (ƙaunar Sarkin Fawan Bakura), da Hajiya Rabi ‘Yar-Akuya. Duka waɗannan matan sun rasu. Ya bar ‘ya’ya takwas, huɗu (4) maza, huɗu (4) mata. Daga cikin ‘yaya maza akwai Aliyu (gidan buwai) da ɗanzomo, da Sama’ila da Wadata, ‘Yabbariya da Nana (nanu), da Luba da Hajara. Cikin maza ɗanzomo da Sama’ila sun rasu.
Domin a ƙara tantance shekarun Makaɗa Alhaji Bawa ɗan’anace, an waiwayi tattaunawar da ya yi da Malam Amadu Sakkwato a gidan rediyon Rima a shekarar 1978, ya bayyana cewa yana da shekaru goma (10) ya fara biyar kawunsa Anace wajen yawon kiɗa. Sannan yana da shekaru talatin da ɗaya (31) da haihuwa, ya fara barin ƙauyensu da ƙauyukan kewansu, zuwa wasu garuruwa da ƙasashe wajen kiɗa. Malam Ango Zariya a tasu tattaunawar (da ɗan’anace) a gidan rediyo RTɓK a shekarar 1972 ya sake maimaita wannan magana ta lokacin da ya fara sana’ar waƙa da kuma sadda ya fara barin gida wajen yawon waƙa.
Malam Aliyu Muhammadu Bawa ɗan’anace da aka fi Sani da Aliyu ɗan Gidan Buwai mai shekaru Hamsin (50) a duniya. Kuma yana daga cikin ‘ya’yan da ɗan’anace ya haifa, ya bayyana cewa, suna tare da Yahaya a lokacin da ɗan’anace yake labarta musu tarihin rayuwarsa da ta sana’arsa ta waƙa. “Saboda haka ni shaidu ne kan maganar shekarun mahaifimmu”
Duk da cewa har zuwa yanzu, hannu bai kai ga aikin Ibrahim Muh’d (1977) “Waƙoƙin Maza na ɗan’anace ba” amma Gusau, (1996) ya ambata aikin Ibrahim, (1977) a cikin littafinsa mai taken Makaɗa da Mawaƙan Hausa na I, kuma aikin Gusau ya zo bayan shekaru goma sha tara (19) da gabatar da aikin Ibrahim, (1977). Wannan tsakure ya aminta da shekarun ɗan’anace sun haura saba’in, ga alama shekarun ɗan’anace sun doshi casin, saboda a zamaninsa ba a samun takardar haihuwa sai dai kintace da kwantace da kirdado da hasashe da aunawa.
ɗan’anace dai shi ɗan fari (ɗa na farko da aka fara haihuwa) ga mahaifansa. Abdullahi Baƙo Mai Jirgi, Bagobiri daga Kagarar-Rima ƙasar Gwaranyo ta Jihar Sakkwato da Malama Aminatu (“Yar-Abu) Bazamfara daga ‘Yartsakkuwa, ƙasar Gandi, Rabah, Jihar Sakkwato sun haifi ‘ya’ya kamar haka: Muhammadu ɗan’anace, Umamaru ɗangigala, Salamatu, Garban Zaɓe, Sama’ila, Inno Uwar Duma, Hafsatu ‘Yardela da Ibrahim Zaɓe. Dukkanin ‘yan uwan haihuwar ɗan’anace sun riga shi rasuwa, sai mutum ɗaya Ummaru ɗangigala wanda yar rasu bayan rasuwar ɗan’anace a shekarar 1970.
2.0
Tarihin Shago a Taƙaice:
An haifi shago a ranar Litinin 18 /01/1914 ya rasu Laraba 2 Nuwamba,1988 yana da shekaru Saba’in da huɗu (74). Sunan shi na yanka Abubakar. Sunan mahaifinshi Aliyu (Bawa). Malam Aliyu Bafulatani ne daga wani ƙauye mai suna magamindiddi a ƙasar maradun, Jihar Zamfara. Daga nan ne sana’ar kiwo tak kawo shi ‘Yakkohoji ta ƙasar Bakura Jihar Zamfara. Sai ya ƙara sana’ar fawa bisa ga tashi ta asali ta kiwo. A wannan lokacin shi Bawa yana kiwo kuma yana shiga runji ya yanka dabba ya sayar da nama. Allah ya haɗa shi da Faɗimatu (jimma) suka yi aure. Ita Faɗimatu (jimma) ɗiyar Galadima ‘Yarkofiji ɗanzarma ce. Kuma ita ce mahaifiyar Shago. Galadiman ‘Yarkofoji ɗanzabarma asalinsa mutumin Bulƙe ne, ƙasar Kuryag Gandi, riƙon Rabah Jihar Sakkwato.
Tun yana ɗan shekara sha biyu (12), Shago ya fara jagorantar wata wasa ta yara matasa masu irin shekarunsa mai suna buga a kama (nau’in kokowa), da kuma wasan woowoo (wasan wuta). Duka waɗannan wasanni da ake yi ga watan shara sai yaro mai kuzari ko mai kankajeli, ko yaro mai ƙarfi a jikinsa ke sha’awa da shiga irin wannan wasanni. Hasali ma, da waɗannan wasannin ake kimtsa yara masu tare ma garururwa da ƙasashensu yaƙi tun farkon ginuwar unguwanni da manyan garuruwa na ƙasar Hausa. Yara masu irin waɗannan wasannin, su ne suke shiga wasannin Tauri, da Dambe da Kokawa.
Laƙabin Shago ya samu ga Abubukar Shago saboda shago na nufin duk abinda ya fuskanci mutum zai tare shi, ko kuma duk abinda mutum ya tunkara zai ima masa ko ya ije shi. To wannan kalma ta shago Hausawa na amfani da ita ga mutane da dabbobi a kan abinda ke nuna ƙarfi da buwaya. Shago tun a wasan matasa ya nuna buwaya domin a kowace wasa in yat ture abokin wasa sai ya kai ƙasa, kuma ba zai tasowa ba sai dai an tadda shi. Da wannan sunan shago ya dallashe sunansa na yanka wato Abubakar.
Abubaka Shago ya mayar da ƙarfin jikinsa da Allah ya bashi wajen raya al’adun kokowa da dambe na matasa, yana yawo a ƙauyukkan da ke kusa ga ‘yarkofoji kamar ƙauyukan ɗankadu, ɗankaiwa, Maɗacci, Damɓu, Birnin Tudu, Hili, Durumba, Maizuma, da ire-irensu. Duk waɗannan ƙauyuka ne da Shago ya kai ziyara domin wasan kokawa da Dambe.
A Shekarar 1943 sai yah hita daga garinsu ‘Yarkofoji zuwa ‘Yartsakkuwa domin su haɗu da Makaɗa ɗan’anace. Bayan haɗuwarsu, zumuntar makaɗi da mowarsa ɗan Dambe taƙ ƙullu har zuwa wafatinsu. A lokacin da suke yawon wasan Dambe, sun zagaya lungu da saƙo na ƙasar Hausa. Haka nan sun tsallaka maƙwabtan Nijeriya kamar ƙasar Nijar, da Burkina Faso wajen wasan Dambe.
Tarihi ya ruwaito Shago ya buga tarihi a wajen wasan dambe kamar haka:
Shago ya buga wasan dambe da Audu kai kaɗai gayya, amma shago ya samu nasarar kashe Audu a watan Mayu 1957 a Kano.
Shago ya buga wasan dambe da ɗandambe Jannasuru, amma shago ya samu nasarar kashe Audu a Jibiya da Sakkwato.
Shago ya buga wasan dambe da Bawan Tarasa, amma shago ya samu nasarar kashe Bawan Taransa a garin birnin Kebbi.
Shago ya buga wasan dambe da Tiri Gurbin Bore, amma Shago ya samu nasarar kashe Tiri a Jibiya, Jihar Katsina.
Shago ya buga wasan dambe da ɗandunawa, a Gusau, amma babu kisa a tsakaninsu Oktoba 1957.
