Daga Ibrahim Muhammad Kano.
Wani ɗan siyasa daga yankin Ungogo yace ya fito neman takara ne don taimakawa al’ummar yankinsa na Ungogo da Minjibir a majalisar tarayya a ƙarƙashin ADC.
Dan takara Hon. Zaharaddin Haruna ya ce idan Allah ya sa ya yi nasara a zaɓen 2027 zai baiwa harkar ilimi da lafiya muhimnanci da kula da matasa maza da mata da sauran fannoni don samun cigaba.
Matsayin da yake nema al’ummar karamar hukumar ne suka buƙaci ya fito ba zaɓin kansa bane, idan Allah ya bashi nasara ba zai ba su kunya ba.
Ya nuna farin cikin sa da shigowar madugun Kwankwasiyya cikin ADC wannan cigaba ne sosai, sannan ya yi fatan Allah ya ƙara wa jam’iyyar karɓuwa.
