Tinubu ya jaddada ƙudurin gyaran tattalin arzikin Nijeriya ga masu zuba jari na duniya a Faransa

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Shugaban Nijeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya gana da manyan masu zuba jari na ƙasashen duniya a Paris, Babban Birnnin ƙasar Faransa, inda ya jaddada aniyarsa ta tabbatar da gaskiya, daidaiton kuɗaze da aiwatar da gyare-gyaren tattalin arziki cikin gaggawa.

Shugaban, wanda ya bar Nijeriya a ranar Lahadi domin wata ziyarar ƙasashe uku, ya bayyana cewa shirin gyaran tattalin arzikin gwamnatinsa ya ƙunshi matakan kawar da tangarɗar tsarin kuɗi tare da daidaita manyan alamu na tattalin arziki, domin shimfiɗa tubalin bunƙasa mai ɗorewa da haɗa kowa da kowa.

Tinubu ya kuma bayyana cewa gwamnatinsa na da niyyar zurfafa gyare-gyare, inganta gaskiya a dukkan matakan harkar man fetur, tare da aiwatar da dabarun tsaro masu faɗi, ciki har da bai wa ‘yan sanda iko a matakin jihohi da kuma katse hanyoyin samun kuɗaɗen ‘yan ta’adda.

A cewarsa, kamar yadda mai magana da yawunsa, Bayo Onanuga, ya bayyana a wata sanarwa ranar Talata, “Babban abin da muka sa gaba shi ne tabbatar da dorewar manufofi da kuma aiwatar da su yadda ya kamata domin ganin sun haifar da anfani ga dukkan ‘yan Nijeriya.”

Wasu daga cikin masu zuba jari da suka halarci taron sun yaba da gyare-gyaren da gwamnatin ke yi, tare da nuna kyakkyawan fata game da makomar tattalin arzikin Nijeriya.

A yayin taron, ɗaya daga cikin masu zuba jarin ya tambayi Shugaban ƙasa game da shirinsa bayan shekarar 2027, inda ya yi alƙawarin ƙarfafa tsauraran ƙa’idojin kula da kuɗi da gaskiya, tare da tabbatar da daidaito a manufofin gwamnati.

Ministan Kuɗi kuma Ministan Tattalin Arziki mai kula da haɗin kai, Taiwo Oyedele, ya bayyana cewa Nijeriya ta samu ci gaban GDP mai ƙarfi a ma’aunin dala a shekarar 2025.

Ya ce ƙasar ta samu ci gaban GDP na kashi 11.2 cikin ɗari a bara, wani sakamako da ke ƙarfafa burin Nijeriya na zama tattalin arzikin dala tiriliyan ɗaya nan da shekarar 2030.

Oyedele ya jaddada cewa babbar manufar gwamnati a halin yanzu ita ce sauya gyare-gyare zuwa sakamako mai anfani ga al’umma, tare da alƙawarin fitar da bayanan kuɗi a kowane wata uku.

A nata ɓangaren, Babbar Daraktar Hukumar Kula da Bashin ƙasa (DMO), Patience Oniha, ta tabbatar wa masu zuba jari cewa gwamnati na tafiyar da harkar bashi cikin tsari da hikima, tare da mayar da hankali kan ɗorewar bashi.

Masu zuba jarin da suka halarci taron sun haɗa da manyan kamfanoni kamar Citibank, Amundi na Faransa ƙarƙashin jagorancin Valerie Baudson, da kuma BlueCrest, Ninety One, Kirkoswald Capital, Principal Finisterre, da kuma kamfanonin Amurka irin su Prudential Global Investment Management (PGIM) da Mesarete Capital.

Wannan ganawa na daga cikin ƙoƙarin gwamnatin Nijeriya na jawo hankalin masu zuba jari na duniya, tare da ƙarfafa amincewa da tattalin arzikin ƙasar a idon duniya.

By ukarofi