Ba ni da wurin zama da ’ya’ya 10, inji matar da aka saki a kotu

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Wata mata mai shekara 44, Zainab Isah, ta bayyana cikin kuka a gaban Kotun Shari’a da ke yankin Magajin Gari a Jihar Kaduna cewa ba ta da inda za ta nufa bayan mijinta ya sake ta, duk da cewa tana da ’ya’ya goma.

Zainab ta shaida wa kotu cewa an aurar da ita tun tana da shekara 14 ga tsohon mijinta, Abdulhamid, inda suka shafe kusan shekaru 30 suna zaman aure tare. “Na haifa masa ‘ya’ya goma, kuma mun zauna lafiya tsawon lokaci,” inji ta.

Ta ƙara da cewa, mijin nata ya sake ta ne a ranar 1 ga Janairu, 2026, amma har yanzu ba ta kammala iddah ba kamar yadda addinin Musulunci ya tanada. “Na zauna lafiya da kishiyoyi na, amma ba zan iya barin ‘ya’yana a hannunsu ba, musamman ganin cewa uku daga cikinsu na fama da rashin lafiya,” inji Zainab.

A ɓangarensa, lauyan mijin, Abdulrashid Musa, ya roƙi kotu da ta umarci matar da ta bar gidan wanda yake wakilta, yana mai cewa an riga an raba aurensu. Ya bayyana cewa mijin ya furta saki sau biyu, inda ya ce an fara yin hakan tun ranar 29 ga Disamba, 2025, kuma ya yi iƙirarin cewa matar ta riga ta kammala iddah. Sai dai, tsohon mijin ya shaida wa kotu cewa a shirye yake ya taimaka wajen biyan kuɗin haya idan matar ta samu sabon wurin zama tare da ‘ya’yanta.

Alƙalin kotun, Mu’awiya Shehu, ya bayyana cewa haƙƙin mace na samun mafaka, abinci da sauran kulawa daga miji na ƙarewa ne bayan an raba aure, yana mai jaddada cewa haƙƙin kula da ‘ya’ya ne kawai ya rage.

Daga nan ne kotu ta ɗage sauraron ƙarar zuwa ranar 1 ga watan Yuni, domin bai wa matar damar neman sabon wurin zama tare da ‘ya’yanta, tare da gabatar da rahoto kan ci gaban da aka samu.

By ukarofi