Hajjin 2026: An shawarci maniyyatan Nijeriya da su gujewa kai miyagun abubuwa ƙasar Saudiyya

Spread the love

Daga DAUDA USMAN a Legas

An shawarci maniyyatan Nijeriya da ke shirin zuwa ƙasa mai tsarki domin sauke farali a bana da su nisanci ɗaukar miyagun ƙwayoyi ko wasu haramtattun abubuwa, domin kauce wa shiga matsala a ƙasar Saudiyya.

Babban Limamin Masallacin Juma’a na rukunin gidajen Unguwar 1000 a Victoria Island, Legas, Malam Suleman Ibrahim, wanda kuma shi ne Shugaban ƙungiyar Izalatul Bid’a Wa Iƙamatus Sunnah (JIBWIS) na Jihar Legas, ne ya bayar da wannan gargaɗi yayin huɗubar Juma’ar makon da ya gabata.

A cikin huɗubar tasa, limamin ya jaddada cewa ya zama wajibi ga dukkan maniyyata su zama jakadun ƙasa nagari, ta hanyar kiyaye dokoki da ƙa’idojin ƙasar Saudiyya, tare da mutunta tsarin da ake bi wajen karɓar baƙuncin al’ummar Musulmi daga sassa daban-daban na duniya.

Ya ce, “Dole ne maniyyata su kare mutuncinsu da kuma martabar Nijeriya, ta hanyar guje wa duk wani abu da zai iya bata sunan ƙasar a idon duniya.”

Limamin ya kuma ja hankalin maniyyatan da su guji aikata duk wani nau’i na manyan laifuka (kabairai) yayin gudanar da ibadar Hajji, tare da tsarkake zukatansu domin samun Hajji karɓaɓɓe (Hajji Mabrur) a wurin Allah.

Haka kuma, ya yi kira ga maniyyata da su yi taka-tsan-tsan wajen hulɗa da wasu daga cikin matafiya a filayen jiragen sama, yana mai gargaɗin cewa akwai wasu da ke amfani da dabaru wajen ɗora wa mutane kayan da ba su sani ba.

A cewarsa, wasu kan nemi a riƙe musu jakunkuna a lokacin tantancewa, su ɓace, sannan idan an samu matsala, mai jakar ne zai fuskanci hukunci.

Saboda haka, ya shawarci maniyyatan da kada su karɓi jakar kowa ko wani kaya daga wanda ba su sani ba, domin kauce wa faɗawa cikin tarkon da zai jefa su cikin matsala.

A ƙarshe, Malam Suleman Ibrahim ya yi addu’ar Allah Ya karɓi ibadun maniyyatan, Ya ba su nasarar sauke farali lafiya, tare da dawo da su gida cikin ƙoshin lafiya.

By ukarofi