Al’ummar garin Masindi da ke ƙasar Uganda sun wayi gari cikin ɗimuwa da al’ajabi bayan da wani mutum da aka bayyana cewa ya mutu ya sake bayyana a garin ’yan awanni kacal bayan an riga an binne gawarsa. Lamarin ya haifar da ruɗani mai tsanani a tsakanin iyalansa da mazauna yankin, inda aka kasa fahimtar yadda abin ya faru.
Rahotanni daga mujallar Daily Monitor ta intanet sun bayyana cewa mutumin mai suna Godwin Baguma, wanda ke zaune a yankin Kijura a tsakiyar Uganda, an ce ya yi ɓatan dabo na makonni da dama kafin daga bisani a gano wata gawa da aka danganta da shi. Wannan ne ya sa iyalansa suka shiga cikin jimami tare da gudanar da jana’iza bayan tabbatar da cewa gawar nasa ce.
Sai dai abin da ya rikita al’umma shi ne yadda bayan kammala binne gawar, daga baya aka gano cewa Baguma yana raye a wani wuri daban a lardin Masindi, lamarin da ya sake jefa iyalansa cikin mamaki da ruɗani, tare da buɗe sabon babi na tambayoyi kan ainihin abin da ya faru.
Bayanai daga da iyalan Baguma wanda aka ce yana da ɗan taɓin hankali ya shiga duniya ba tare da sanar da kowa ba abin da ya janyo aka tashi neman sa ruwa a jallo.
Al’amarin ya ya sauya a ƙarshen mako lokacin da iyalansa suka sami bayanai daga ’yan sanda cewa sun samo wata gawa da ta ruɓe daga gonar rake a Kisanja ranar Juma’a.
An kai gawar zuwa ɗakin ajiye gawa a asibitin Masindi inda aka bayar da sanarwar samun gawar ga duk iyalan da ke neman wani nasu da su je su duba.
Mahaifin Baguma, Yakobo kamuturaki ya ce bayan samun sanarwar ne ranar Lahadi, sai ya aiki ’ya’yansa zuwa mutuwaren domin tabbar da ko gawar ta ɗansa ne da ya ɓace. Kuma bayan yin duban tsanaki kan gawar sai suka koma gida suka tabbatar wa mahaifinsa cewa gawar ta ɗansa ce Baguma.
“An faɗa cewar gawar ta ɓaci. ’Ya’yana sun je kuma sun gano ɗan uwansu. Mun yarda da abin da suka faɗa sannan mun amince da cewa ya mutu,” inji Kamuturaki.
Bayan samun wannan bayanin ne sai iyalansa dandanan suka gaggauta yi masa jana’iza saboda yadda ta zagwanye. Labarin rasuwar Baguma ya yaɗu kamar wutar daji a garin Kijura da kewaye al’amarin da ya sa jama’a suka yi ta tururuwa domin taya iyalansa alhini.
An gudanar da jana’izarsa ranar Lahadi inda iyalan suka shirya yin jana’izar bankwana da mamaci washegari wato ranar Litinin.
To sai dai kuma abin da aka fara a cikin alhini ya sauya zuwa ruɗani da mamaki bayan fitowar rahotanni da ke cewa Baguma yana raye a Kihanguzi da ke garin Labongo a lardin Masindi.
“Da farko mun yi biris da labarin. Tuni mun binne shi. Amma kuma sai muka yanke cewa mu je mu binciki gawar,” inji ’yar uwar Baguma, Jane Birundi.
Jane ta ce iyalan Baguma sun garzaya zuwa wurin kuma suka samu Baguma a raye. Rahotanni sun ce Baguma yana kwana a gidan abokinsa.
“Lokacin da muka gan shi, mun kaɗu. Ba mu yarda shi ne a raye ba,” inji Birungi.
Ba tare da ɓata lokaci ba sai aka mayar da Baguma gida.
Abin da ya faru ya sanya iyalan Baguma dandanan suka tono gawar mutumin da suka binne sannan aka mayar da gawar zuwa mutuwaren asibitin Masindi.
