Gwamna Dikko Raɗɗa ya buƙaci maniyyata su yi wa Jihar Katsina addu’a

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Raɗɗa, ya yi kira ga dukkan maniyyatan Hajjin bana da su yi addu’a domin samun zaman lafiya mai ɗorewa, haɗin kai da tsaro a Jihar Katsina da ma ƙasa baki ɗaya.

Gwamnan ya bayyana hakan ne a yayin bikin bankwana da maniyyatan jihar Katsina zuwa ƙasar Saudiyya domin gudanar da aikin Hajji.

Radda ya jaddada ƙudirin gwamnatinsa na tabbatar da an gudanar da aikin Hajji cikin tsari, daidaito da kuma samun cikakkiyar fa’idar ibada.

“Hajji na ɗaya daga cikin rukunan Musulunci guda biyar, kuma yau rana ce mai albarka ga kowa da kowa. Waɗanda Allah ya zaɓa domin sauke wannan ibada mai girma,” in ji gwamnan.

Ya bayyana cewa gwamnatin jihar ta shiga tsakani domin magance matsalolin kuɗi da suka taso da farko wajen cike guraben Hajji.

“An sanar da ni cewa jihar ta fuskanci ƙalubale wajen cike guraben Hajji da aka ba ta. Saboda haka muka amince da bayar da rance na naira biliyan 3.8, wanda ya ba mu damar cike gurabe 3,890 na Hajjin bana,” ya bayyana.

Haka kuma gwamnan ya sanar da cewa gwamnatin jihar Katsina za ta ɗauki nauyin kuɗin hadaya ga dukkan maniyyatan Hajjin 2026, a matsayin wani ɓangare na kulawa da jin daɗinsu.

Ya kuma bayyana cewa kowanne maniyyaci zai samu dala 500 domin tallafa masa wajen buƙatun yau da kullum a ƙasa mai tsarki.

Gwamnan ya ƙara da cewa an tura jami’ai 200 domin kula da tafiyar Hajji yadda ya kamata, tare da samar da jagoranci na addini, lafiya da kuma ayyukan gudanarwa.

“An zaɓi waɗannan jami’ai ne bisa cancanta domin tabbatar da kula da maniyyata ta fuskar addini, lafiya da kuma sauran buƙatu,” in ji shi.

Ya kuma bayyana cewa gwamnatinsa ta ƙarfafa tsarin aiki na Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Katsina domin inganta aiki da kuma magance matsalolin da suka faru a baya.

“Haka nan na umarci Amirul Hajj da sauran masu ruwa da tsaki da su tabbatar da tsauraran matakan kulawa, gaskiya da ladabi a tsakanin jami’ai,” ya ƙara da cewa.

Malam Dikko Raɗɗa ya shawarci maniyyata da su zama jakadu nagari na jihar Katsina, yana mai tunatar da su irin sadaukarwar da iyalai suka yi domin su samu damar zuwa Hajji.

“Mutane da dama sun sayar da dukiyoyinsu domin yin Hajji. Saboda haka ana sa ran za ku nuna kyakkyawan ɗabi’a, haƙuri da mutunta juna,” ya gargade su.

Haka kuma ya ja hankalinsu da su guji yaɗa jita-jita ko bayanan da za su ɓata sunan gwamnati yayin aikin Hajji.

Gwamnan ya kuma bayyana cewa an samu gagarumin ci gaba a fannoni na masauki da abinci ga maniyyata a ƙasa mai tsarki.

“Tun bayan hawana mulki, mun tabbatar da inganta masauki da abinci ga maniyyatanmu. Na kai ziyara da kaina a baya kuma na gamsu da ci gaban da aka samu,” ya ce.

Ya yabawa Hukumar Jin Daɗin Alhazai da sauran hukumomi bisa ingantaccen aiki da suka nuna.
Gwamnan ya ƙara da jaddada cewa aikin Hajji wata babbar dama ce ta ibada, yana mai kira ga maniyyata da su riƙe nagarta, haƙuri, gaskiya da haɗin kai.

By ukarofi