Gwamnatin Tarayya ta soke jarrabawar shiga kwalejin ilimi

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Gwamnatin Tarayya ta sanar da cire sharadin rubuta jarabawar UTME ga ɗaliban da ke neman shiga makarantun kwalejin ilimi.

Ministan Ilimi, Tunji Alausa ne ya bayyana hakan a Abuja yayin taron tsara manufofin shiga jami’o’i da sauran manyan makarantu na shekarar 2026.

Ya ce daga shekara mai zuwa, ɗaliban da suka samu aƙalla kredit huɗu a darussan da suka dace za su iya neman shiga shirin NCE ba tare da sun rubuta UTME ba.

Sai dai ya bayyana cewa dole ne irin waɗannan ɗalibai su yi rajista da hukumar JAMB, domin tantance takardunsu kafin a ba su gurbin karatu ta tsarin CAPS.

Alausa ya ce gwamnatin ta ɗauki matakin ne domin faɗaɗa damar shiga makaranta, rage matsin lambar UTME, da kuma ƙarfafa sha’awar harkar koyarwa da fannin noma.

Haka kuma, gwamnatin ta ce ta ba da irin wannan sassauci ga masu neman gurbin karatu na babbar Diploma a wasu darussan noma da ba na fasaha ba.

By Babaji