Hamza Mai Bulawus ya lashe zaɓen fidda gwani na SDP a Zamfara

Spread the love

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau

Alhaji Hamza Musa Mai Bulawus ya lashe zaɓen fidda gwani na jam’iyyar Social Democratic Party (SDP) a Jihar Zamfara ba tare da hamayya ba.

Zaɓen fidda gwanin an gudanar da shi ƙato bayan ƙato a dukkan mazaɓu 147 dake a ƙananan hukumomi 14 na jihar.

Mai Bulawus ya samu jimillar ƙuri’u 36,556.

Da yake sanar da sakamakon a Gusau a yau Talata, jami’in yaɗa sakamakon zaɓen fidda gwani na jam’iyyar SDP a Jihar Zamfara, Bello Hussaini Gusau, ya ce an gudanar da zaɓen ne a ƙarƙashin ikon hedikwatar jam’iyyar ta ƙasa.

“Dangane da ikon da hedikwatar jam’iyyar ta ba ni a matsayin jami’in kula da zaɓen fidda gwani na jam’iyyar SDP, na ayyana Hamza Musa Mai Bulawus a matsayin wanda ya lashe zaben fidda gwani na jam’iyyar a Jihar Zamfara,” in ji Hussaini.

Nasarar da babu hamayya ta sanya Mai Bulawus a matsayin wanda zai tsaya takarar gwamnan jihar Zamfara a zaɓen 2027.

Jam’iyyar ta ce an shirya zaɓen fidda gwani kai tsaye ne domin tabbatar da cewa ‘yan jam’iyya sun samu halartar a faɗin jihar da kuma tabbatar da haɗin kai kafin babban zaɓen.

By ukarofi