EBOLA: Rigakafi ya fi magani

Spread the love

Yayin da cutar Ebola (EVD) ke sake ɓulla a Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Kongo (DRC) tare da tabbatar da samun wani mutum da ya shigo da cutar a maƙwabciyar ƙasar Uganda, duniya ta sake shiga yanayin fargaba da taka-tsantsan. 

Wannan lamari ya sake tunatar da al’ummar duniya cewa cututtuka masu yaɗuwa ba sa mutunta iyakokin ƙasashe, kuma sa ido da shiri tun kafin matsala ta auku su ne manyan makaman kariya daga annoba.

Da take fahimtar girman barazanar da lamarin ke haifarwa, Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta ayyana ɓarkewar cutar a matsayin Gaggawar Lafiyar Jama’a Ta Duniya (PHEIC). Ko da yake wannan mataki bai kai matsayin ayyana annoba ta duniya ba, amma yana nuna muhimmancin lamarin da kuma buƙatar haɗin gwiwar ƙasashe domin daƙile yaɗuwar cutar.

Bayanan da ke fitowa daga Kongo sun nuna cewa an riga an samu sama da mutum 1,000 da suka kamu da cutar, yayin da fiye da mutum 80 suka rasa rayukansu sakamakon nau’in cutar na Bundibugyo, musamman a lardunan Ituri da North Kivu. Waɗannan alƙaluma suna da matuƙar tayar da hankali, kuma suna nuna muhimmancin ɗaukar matakan kariya tun da wuri, musamman ga ƙasashen da ke da alaaar zirga-zirga da kasuwanci da yankunan da annobar ta shafa.

Abin farin ciki, Nijeriya ta nuna ƙwazo wajen tunkarar wannan barazana. Cibiyar Kula da Cututtuka da Rigakafi ta Nijeriya (NCDC) ta ƙaddamar da matakan sa ido na gaggawa a faɗin ƙasar tare da ƙarfafa bincike da tantance matafiya a filayen jiragen sama, kan iyakokin ƙasa da sauran hanyoyin shiga Nijeriya. Haka kuma, cibiyar tana aiki kafaɗa da kafaɗa da Sashen Kula da Lafiya a Tashoshin Shiga ƙasa (Port Health Services) domin tabbatar da cewa duk wani matafiyi da ya fito daga yankunan da cutar ta ɓulla ya fuskanci cikakken bincike.

Har ila yau, NCDC ta kunna cibiyoyin binciken ƙwayoyin cuta na ƙasa tare da ƙarfafa tsarin sa ido kan cututtukan zubar jini, matakin da ke nuna cewa Nijeriya na ƙoƙarin gano duk wata alamar cutar tun kafin ta bazu.

Hukumar ta kuma fitar da shawarwari masu amfani ga jama’a. An buƙaci ’yan ƙasa da su kula da tsafta ta hanyar wanke hannu akai-akai, guje wa hulɗa da dabbobin da suka mutu ko naman daji da ba a san asalinsu ba, tare da kauce wa tafiye-tafiyen da ba dole ba zuwa ƙasashen da cutar ta ɓulla. Haka kuma, an gargaɗi ma’aikatan lafiya da su kasance cikin shiri tare da bin ƙa’idojin kariya daga kamuwa da cututtuka, tare da killace duk wanda ake zargi da alamun cutar da tarihin tafiya zuwa yankunan da abin ya shafa.

Waɗannan matakai sun cancanci yabo. A ƙarƙashin jagorancin Dakta Jide Idris, NCDC ta nuna shirinta da ƙwarewarta wajen fuskantar barazanar lafiyar jama’a. Sai dai rashin samun wanda ya kamu da cutar a Nijeriya a halin yanzu bai kamata ya sa a yi sakaci ba. Yawan al’ummar ƙasar, kusancinta da sauran ƙasashen yankin da kuma yawan zirga-zirgar matafiya daga sassa daban-daban na duniya na nufin cewa shiri ba zaɓi ba ne, wajibi ne.

Nasarar da Nijeriya ta samu wajen daƙile Ebola a shekarar 2014 har yanzu tana daga cikin manyan nasarorin da ƙasar ta samu a fannin lafiyar jama’a. Darussan da aka koya daga wannan ƙwarewa su ne ya kamata su zama jagora a yau. Gano cutar da wuri, bin diddigin waɗanda suka yi hulɗa da masu ɗauke da ita, wayar da kan jama’a da kuma isar da sahihan bayanai cikin gaskiya su ne suka taimaka wajen cimma wannan nasara.

Saboda haka, gwamnati dole ta ci gaba da ƙarfafa matakan da take ɗauka. Ya kamata a faɗaɗa shirye-shiryen wayar da kan jama’a ta kafafen yaɗa labarai na gargajiya da na zamani domin tabbatar da cewa sahihan bayanai sun isa kowane yanki na ƙasar. Haka kuma, akwai buƙatar yaƙi da yaɗa ƙarya da jita-jita, domin irin waɗannan bayanai na iya haddasa firgici marar amfani tare da raunana amincewar jama’a ga hukumomin lafiya.

A ƙarshe, hana Ebola shiga Nijeriya ba aiki ne na gwamnati kaɗai ba. Hukumomin gwamnati, ma’aikatan lafiya, kafafen yaɗa labarai da kuma talakawan ƙasa duk suna da rawar da za su taka. Nijeriya dole ta kasance cikin shiri, taka-tsantsan da haɗin kai.

A harkokin lafiyar jama’a, gaskiya ɗaya ce ba ta sauyawa, wato; rigakafi ya fi magani, kuma ya fi magani araha da sauƙin aiwatarwa.

By ukarofi

Leave a Reply