Sojoji sun kashe ‘yan ta’adda 50 har da babban kwamandan ISWAP

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja 

Dakarun Operation Haɗin Kai sun ƙara ƙaimi wajen yaƙi da ta’addanci a yankin Arewa maso Gabas, inda suka kashe sama da ‘yan ta’adda 50, ciki har da wani babban kwamandan ƙungiyar ISWAP, tare da kama wasu da ake zargi da taimaka musu a Jihar Borno.

Rahoton ayyukan soji da Kamfanin Dillancin Labarai na ƙasa (NAN) ya samu a Abuja ranar Laraba ya bayyana cewa wannan nasara ta samu ne bayan wani hari ta sama da aka kai daidai kan sansanonin ‘yan ta’adda da ke yankunan Kirta da Arina Ciki.

Rahoton ya ce harin ya yi sanadiyyar kashe wasu manyan kwamandojin ‘yan ta’adda, ciki har da Khalifa Umar, wanda ke cikin Majalisar Shura ta ƙungiyar ISWAP.

A cewar rahoton, ci gaba da kai hare-haren sama ya tilasta wa ‘yan ta’addan barin maɓoyarsu da ke tsibirai tare da komawa yankunan babban kasa saboda matsin lambar da suke fuskanta daga sojoji.

Rahoton ya kuma bayyana cewa dakarun sun kama mutane uku da ake zargi da samar wa ISWAP kayan aiki da bayanan sirri, tare da kama wani soja da ya gudu daga aiki ɗauke da makaminsa, wanda daga baya aka alaƙanta shi da aikata wasu laifuka a Maiduguri da kewaye.

An ƙwato bindiga tare da harsasai, mota, lita 30 na man fetur, da wasu kayayyakin da ake zargin ana amfani da su wajen tallafa wa ayyukan ta’addanci.

Yankin Arewa maso Gabas na ci gaba da kasancewa cibiyar yakin da Nijeriya ke yi da ƙungiyoyin ta’addanci karkashin Operation Hadin Kai.

A cikin shekaru da suka gabata, hare-haren haɗin gwiwa na sama da kasa sun mayar da hankali kan sansanonin ISWAP da JAS da ke yankin Tafkin Chadi da dajin Sambisa.

Jami’an soji sun ce wannan sabon salon yaki ya tilasta wa ‘yan ta’adda wargajewa zuwa ƙananan ƙungiyoyi, lamarin da ya ƙara sauƙaƙa musu kamuwa da hare-haren dakarun tsaro.

Sojojin sun jaddada cewa za su ci gaba da gudanar da irin waɗannan ayyuka domin ara raunana karfin ‘yan ta’adda da kuma dawo da zaman lafiya a yankin.

By ukarofi

Leave a Reply