Daga DAUDA USMAN a Legas
Al’ummar Musulmi dake zaune a yankin Mile 12 International Market dake Jihar Legas sun gudanar da Sallar Idi cikin kwanciyar hankali da lumana, tare da yin addu’o’i na zaman lafiya da ci gaban ƙasa.
Bayan tabbatar da ganin jinjirin watan Zulhijja a sassan duniya da Nijeriya baki ɗaya, Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Sa’ad Abubakar III, ya ayyana ranar Laraba a matsayin ranar Babbar Sallah, inda Musulmai suka gudanar da Sallar Idi tare da shagulgulan murnar wannan babbar rana.
A Mile 12 International Market, al’ummar Musulmi sun gudanar da Sallar Idi a filin makarantar firamare ta Maidan Primary School, inda Sheikh Malam Ibrahim Aliyu Mai Dubu-Dubu, Mataimakin Limamin Babban Masallacin Juma’a na ’Yan Izala da ke kasuwar Mile 12, ya jagoranci sallar.
Daga cikin manyan malaman addini da suka halarci sallar akwai Sheikh Malam Muhammadu Guri, shugaban ƙungiyar Izala ta Mile 12; Sheikh Malam Abdulnasir Usman Mile 12, Limamin Masallacin Juma’a da ke Jackson, Ikeja; Alhaji Dauda Kunkumi, shugaban kwamitin Babban Masallacin Juma’a na Mile 12; Sheikh Malam Aliyu Gombe; Sheikh Malam Tasi’u, Mataimakin Limamin Masallacin Juma’a na ’Yan Shinkafa; da kuma Sheikh Malam Idris As-Salafiyya, tare da sauran manyan malamai da shugabannin al’umma.
Da yake gabatar da hudubar Idi bayan kammala sallar, Sheikh Malam Ibrahim Aliyu Mai Dubu-Dubu ya yi kira ga Musulmi da su ci gaba da ƙarfafa zumunci, haɗin kai da kyakkyawar mu’amala da ’yan uwa, maƙwabta da sauran al’umma, musamman a wannan lokaci na bukukuwan Sallah.
Ya kuma jaddada muhimmancin taimakon juna, haƙuri da zaman lafiya domin ci gaban al’umma da ƙasa baki ɗaya.
A nasa jawabin, shugaban Kasuwar Mile 12 International Market, Alhaji Shehu Usman Jibrin Samfam, wanda kuma shi ne Danlawan Egbaland, ya bayyana farin cikinsa kan yadda aka gudanar da bukukuwan Babbar Sallah cikin lumana.
Ya yi kira ga al’ummar kasuwar da su ci gaba da zaman lafiya da sauran ƙabilun da ke zaune a Jihar Legas, yana mai cewa zaman lafiya shi ne ginshiƙin ci gaba da bunƙasar tattalin arziki.
Haka kuma, ya shawarci direbobi da masu amfani da ababen hawa da su yi taka-tsantsan yayin zirga-zirga a lokacin bukukuwan Sallah domin kauce wa haɗurran da kan haddasa asarar rayuka da dukiyoyi.
Alhaji Shehu Usman Jibrin Samfam ya yi addu’ar Allah Ya karɓi ibadun al’ummar Musulmi, Ya kuma dawo da irin wannan rana cikin ƙoshin lafiya da zaman lafiya a Nijeriya baki ɗaya.
