
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Gwamnatin Tarayya ta tabbatar wa ‘yan Nijeriya cewa tana ƙoƙarin ganin cewa an ceto ɗalibai da malaman da aka sace a jihohin Oyo da Borno, tana mai bayyana cewa manufarta ita ce ceto su cikin ƙoshin lafiya da kuma kawo ƙarshen ta’addanci a sassan ƙasar.
A cewarta, hukumomin tsaro suna ɗaukar halastattun matakai wajen ceto waɗanda suke hannun ‘yan ta’adda da tabbatar da kama masu hannu a ciki.
Haka na zuwa ne yayin da al’ummar ƙasa suke cigaba da nuna damuwa akan sace kimanin ɗalibai 82 tsakanin 13 da 15 ga Mayu a Oyo da Borno.
A jihar Borno, ‘yan bindiga sin yi awon-gaba da ɗalibai 42 a makarantun ƙananan hukumomin Askira-Uba da Chibok a ranakun 13 da 14 na watan Mayu.
Haka ma a Oyo, inda aka sace wasu ɗalibai 40 a ranar 15 ga Mayu a makarantun nazare da firamare ta Baptist, Yawota; Community Grammar School da L.A. Primary School, Esiele waɗanda ke Ƙaramar Hukumar Oriire.
Da yake ganawa da manema labarai a Abuja, Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da kan Al’umma, Mohammed Idris ya bayyana hare-haren a matsayin “cin zarafi na kai-tsaye” ga goben Nijeriya.
A jawabin da ya gabatar a madadin Shugaba Bola Tinubu, Minista Idris ya tabbatar wa al’ummar Nijeriya cewa hukumomin tsaro na aiki tuƙuru wajen ɗaukar dukkan matakan da suka dace na ceto mutanen da al’amarin ya shafa.
A cewarsa, Shugaba Tinubu ya umarci dukkan hukumomin tsaro da su yi amfani da dukkan wani salo na doka wajen ceto ɗalibai da malaman da aka sace a jihohin.
