Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Majalisar Wakilai ta Tarayyar Nijeriya ta amince da rahoton da ya shafi kafa rundunar ’yan sandan jihohi tare da amincewa da wasu tanade-tanaden gyaran Kundin Tsarin Mulkin Nijeriya guda 18.
An cimma wannan matsaya ne a zaman majalisar da aka gudanar ranar Alhamis ƙarƙashin jagorancin Kakakin Majalisar Wakilai, Tajudeen Abbas.
Tanade-tanaden da aka amince da su na daga cikin shawarwarin da ’yan majalisar suka yi nazari a kansu yayin tattaunawar da ake yi kan gyaran Kundin Tsarin Mulki, da nufin ƙarfafa shugabanci, inganta tsaro da kuma bunƙasa aikin hukumomin gwamnati a faɗin ƙasar.
Amincewar da majalisar ta yi da rahoton kafa ’yan sandan jihohi na zuwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da kira daga sassa daban-daban na ƙasar na a sake fasalin tsarin tsaro, ta hanyar bai wa jihohi damar kafa rundunonin ’yan sanda na kansu domin tunkarar matsalolin tsaro da suka addabi yankuna daban-daban.
Sai dai zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, Majalisar Wakilai ba ta fitar da cikakkun bayanai kan tanade-tanaden gyaran Kundin Tsarin Mulkin guda 18 da aka amince da su ba.
Ana sa ran za a bayyana ƙarin bayanai nan gaba kaɗan yayin da majalisar za ta ci gaba da bayyana sakamakon zaman nata.
