Daga ALI ABUBAKAR SADIQ
Trump ne da kansa ya bayyana wa duniya cewa, sauran awa guda kacal ya rage ya bayar da umarnin kai wa Iran farmaki, amma ya dakatar sakamakon, a cewarsa, ƙasashen yankin Gulf ne suka nemi alfarmar haka, saboda ana samun ci gaba sosai wajen tattaunawar sulhu da Iran. Wasu majiyoyin sun nuna cewa, wannan rabin gaskiyar maganar ce, domin akwai wani bayanin na sirri da ya tilasta wa Amurka dakatawa da kai harin.
Iran dai ta yi gum da bakinta, inda kawai abinda ta ce shine, da zarar an kai mata hari za ta mayar da martani, wanda zai buɗe wata sabuwar da’ira ta kai harin. Abin ɓoyen da ake zaton ya tilasta Amurka dakatawa shine, yadda a tsakar rana babu wata ƙumbiya-ƙumbiya, Iran ta fito da sabon makaminta na EMP Bomb, wanda ta girke shi a wani wuri yadda tauraron ɗan adam na leƙen asirin Amurka da Israila za su iya ganin sa da tabbatar da shi. Hotunan wannan makamin ya ɗauki numfashin ƙasashen biyu, domin a hasashe, duk da ana zaton Iran na aikin ƙera wannan makami, sai nan da shekaru za su iya samar da shi. Ashe-ashe tuni Iran sun ƙera shi.
Wannan makamin na EMP, da zarar an harba shi, ba zai rushe gini ba, ba zai halaka ɗan adam ba, amma illar da zai yi ta ninka haka. Wato da zarar ya fashe, zai samar da wani haske mai ƙarfi da zai watsa zaruruwan lantar-maganaɗisu (electromagnetic energy), wanda nan take zai gurgunta, ya wargaza da tarwatsa kayan da ke dogaro da aiki da lantarki: Misali; zai rushe tashar wutar lantarki ta hanyar tumbuɗin lantarki a turakun da ke dakon wuta na falwaya da jawo ambaliya cikin turansifomomi su ƙone ya jawo ɗaukewar wutar lantarki na dogon lokaci. Sannan nan take zai ƙone kayan da suka dogara da ‘semi-conducters’ irinsu wayoyin hannu, kayan aikin asibiti, kayan amfani a gidaje irinsu talabijin da kwamfutoci. Sannan zai tsayar da motocin zamani da suka ta’allaƙa da ‘microprocessors’. Haka nan zai tsayar da mahimman harkokin irinsu ayyukan banki da na sadarwa irinsu tangaraho, talabijin da rediyo.
Wannan ne ainihin dalilin da ake tsammani ya dakatar da kai wa Iran hari a wannan kwanaki. A kullum abinda Iran ke burge ni da su shine, yadda suke ba mu darasi, domin mu farka mu gane cewa, babu wani sirri na ƙarfi da nasara a duniya irin ilimi, ginshiƙi da sharaɗin farko a Musulunci, wanda muka yi watsi da shi a yau a matsayin al’umma.
Malam Ali manazarci ne a Kano
