Daga JAMIL GULMA a Kebbi
Rundunar ƴan sandan jihar Kebbi ta sanar da kama waɗansu mutane huɗu bisa zargin yi wa Alhaji Aminu Jega barazanar ya biya Naira Miliyan talatin (30m) a matsayin kuɗin fansa ko kuma su yi garkuwa da shi.
Kakakin rundunar ƴan sandan jihar SP Bashir Usman ya bayyana cewa duk da ya ke sun sakaya lambar da su ke kiran sa da kuma muryar da su ke kiran sa rundunar ƴan sandan ta sami nasarar kama su.
Waɗanda aka kama sun haɗa da Muhammad Shafiu shekaru 21, Mansur Ibrahim shekarau 21, Aliyu Umar shekaru 25, da kuma Muhammad Suleiman mai shekaru 23, bayan da Alhaji Aminu Garba Jega ya kai rahoton ana yi masa barazanar ko dai ya ba su Naira Miliyan talatin (₦30,000,000) ko kuma a yi garkuwa da shi.
Binciken da rundunar ƴan sandan ta gudanar ya bayyana cewa Muhammad Shafiu, Mansur Ibrahim , Aliyu Umar su ne suka nemo layin wayar da Muhammad Suleiman ya ke sauya murya zuwa muryar fulani yana kiran Aminu Jega.
Binciken ya gano cewa ɗaya daga cikin makusantan Alhaji Aminu Jega ne ya nemo musu lambar da kuma sauran bayanan yadda za a gudanar da aikin.
Ya ce an sami nasarar kama su ne a ƙauyukan Gumbin Kure da Gameji da ke ƙaramar hukumar Maiyama kafin su aiwatar da ƙudurin su.
Ya ce rundunar ƴan sandan jihar Kebbi ƙarƙashin jagorancin kwamishina Umar M. Hadejia a shirye ta ke wajen ganin ta kare rayuka da dukiyar al’umma, kuma babu sasaauci ga duk wani ɗan ta’adda.
