Ko akwai waɗanda ƙasa ba ta cin jikinsu bayan binnewa?

Spread the love

Daga ALI ABUBAKAR SADIK

Shin ko akwai waɗanda ƙasa ba ta cin jikinsu bayan binnewa? Tambayar da Shehil Islami Malam Aminu Bello ya jeho kenan. Da farko akwai bukatar a fahimci fadar Allah cikin Suratul Al Rahman cewa; “Dukkan abinda ke kanta (Duniya) mai ƙãrewa ne. Kuma Fuskarar Ubangijinka, Mai girman Jalala da karimci, ita ce take wanzuwa.”

Wannan aya cike ta ke da kimiyya da tauhidi. A kimiyance babu wata halitta da ta ke dorewa a Doron Duniya, domin Allah ya tsara duniyar yadda komai na cakuduwa da sabuntawa da karewa. Daga kasa aka halicci duk masu Rai Kuma cikinta su ke komawa. Ita kanta uwa ma bada maman, wato kasa, sai ta kare ta daidaice tamkar ba a yi ta ba.

Life cycle, wato juyawar rayuwa na canza sinadarai daga mara sa Rai su samar da Mai Rai, su mutu su koma marasa Rai. Wannan jujjuyawa ta dogara ga mahimman abubuwa guda biyu; wato kwayar bacteria da iskar oɗygen. Wadannan abubuwa su ke sa jiki (organic) ya rube ya zama mara Rai (inorganic). Ta haka babu wani abu mai wanzuwa dindindin face zatin ubangiji, domin shi kadai ne Mai halittawa, duk abin halitta kuma fararre ne kararre.

Game da tambayar kuwa, akwai jikuna na halitta da ke daukar tsawon lokaci ba su rube zuwa sinadarai ba. Ba mutane kadai ba har ma da dabbobi. Idan gawa ta sami kabari wanda babu iskar oɗygen ko bacteria zai iya dadewa sosai jikin Bai rube ba. A nan Duniya, a shekarar 2024, masana a Oklahoma sun ci karo da wata fata ta kadangaru irin na da can wanda gwaji ya nuna cewa fatar ta shekara miliyan 290 da binnewa. Wannan ne bangare na wata halitta mafi tsufa da aka taba samu. Ta dau wannan shekaru ba ta rube sakamakon wajen binniyar tata a cikin dagwalon Mai ya ke.

Sannan cikakkiyar Dabba da surorinta gaba daya ba su rube ba, an same ta a Siberia cikin kabarin kankara. Ita wanna Dabba wata irin Giwa ce wadda a yanzu babu irinta duk sun kare, wadda ake kira da mammoth, ta na da gashi duk jikinta da lankwasashshen haure. Wannan giwa ta kai shekaru 50,000 da binnewa, amma saboda samun yanayi na kankara wanda tsananin sanyin ya daskarar da kwayoyin bacteria da iskar oɗygen, ya sa ko kadan wannan Dabba ba ta rube ba. 

Don haka a mutane ma, akan sami wasu gawawwaki da su ka sami wajen binniya Mai karancin bacteria da iskar oɗygen, su kan dau lokaci ba su rube ba. A yanzu haka da za a saka gawa a harba ta sararin sama (space) zata iya miliyoyin shekaru garau saboda babu bacteria da iskar oɗygen a space.

Don haka ba wata karama ba ce idan gawar wani mutum an ganta fresh ba ta rube ba. Fahimtarmu ce da son mu’ujiza ya ke kawo wannan tunani. Amma abinda ya kamata mu tambayi kan mu shine, idan har samuwar hakan wata mu’ujiza ce me yasa ba a taba samun gawar wani Annabi ba? Kuma me ya sa aka sami ta Fir’aunoni da dama?

Misrawa (Egyptians) sun dade da gane tasirin bacteria da iska wajen rubewar gawa, shi ya sa su ke amfani da tsarin sunduki (embalment) wadda ke sa gawa ta Dade ba ta rube ba. Abinda su ke yi shine amfani da wani gishirinsu (natron) wanda ke taimakawa wajen tsotse duk wani ruwa a jikin fata ko tsoka. Idan babu ruwa to bacteria ba za ta iya hayayyafa ba. Sannan su na cire sassn jiki irinsu zuciya, hanta, koda, hanji da kwakwalwa da shafe jikin da wasu sinadarai. A irin firaunoninsu, mafi tsufa da aka tono su ne wanda aka fara tonowa a shekarar 1881, gawar Merenre na ɗaya, wanda ta kai shekaru 4,300 da binnewa. Sai kuma gawar Hakeshepes, wadda aka tono 2023 ita ma shekarunta 4,300. Sannan akwai shahararriyar gawar fir’auna Tutankhamun wadda aka tono a shekarar 1922 cikin akwatuna na zinare guda uku, wata daya cikin daya. Ita Kuma shekarun ta 3,300. Duk wadannan sun girmi gawar Fir’aunan Annabi Musa, wato Ramses. Merenre I da Hakeshepes sun girmi zamaninsa da shekara dubu, yayinda Tutankhamun ya mutu da shekaru 44 sannan Ramses ya hau sarauta. 

Binciken kimiyya wanda masana kimiyya sama da 100 suka gudanar kan gawar Ramses a kasar Faransa a shekarar 1976 (cikinsu har da Maurice Bucaile wanda ya musulunta) sun nuna cewa Ramses a ruwa ya mutu saboda samun gishirin teku a jikinsa. Kamar yadda Allah, shekaru 1400, ya yi busharar cewa; Q10:92:  To, a yau Munã kuɓutar da kai game da jikinka, dõmin ka kasance ãyã ga waɗanda suke a bãyanka. Kuma lalle ne mãsu yawa daga mutãne, haƙĩƙa, gafalallu ne ga ãyõyinMu.”

A takaice mu gane cewa babu wata mu’ujiza ga samun gawa ba ta rube ba. Domin da an sami Annabawa. Maimakon haka sai ga shi manyan kafirai ne gawawwakinsu su ka iso gare mu.

Malam Ali Abubakar manazarci ne a birnin Kano – Nijeriya

By ukarofi

Leave a Reply