Abin mamaki da takaici ne yadda farashin man fetur ya ragu ƙwarai, amma har yanzu wasu dillalan mai sun ƙi sauke farashinsa. Sun ƙi bin sauyin da ya faru, suna ci gaba da sayar da mai yadda suka ga dama.
Abin lura shi ne, idan farashin mai ya tashi, ba sa ɓata lokaci wajen ƙara farashi. Amma idan ya sauka, sai su yi kunnen uwar shegu, kamar ba su san abin da ke faruwa ba.
Mu dai addu’armu ita ce Allah Ya hana duk wanda yake son ganin mun shiga ƙunci cimma burinsa. Tashin farashin da aka sha fama da shi ya ragu, don haka muna fatan waɗannan dillalai za su tausaya wa al’umma su sauke farashin mai yadda ya dace.
Allah Ka sanya su sassauto. Idan kuma suka ƙi, Allah Ka hana su ci gaba da gallaza wa talakawa. Amin.
Daga: Mukhtar Ibrahim Saulawa, Katsina. 07066434519/08080140820.
