
Magajin garin New York, Zohran Mamdani, ya ce gwamnatin birnin na duba yiwuwar kama Firaministan Isra’ila, Benjamin Netanyahu, idan ya halarci babban taron majalisar ɗinkin duniya (UNGA) da za a gudanar a watan Satumba.
Mamdani ya bayyana hakan ne yayin wata hira da jaridar The New York Times, inda ya ce sashen shari’a na birnin na nazarin ko akwai hurumin aiwatar da sammacin kama Netanyahu da Kotun Hukunta Manyan Laifuka ta Duniya (ICC) ta bayar.
Ya bayyana Netanyahu a matsayin wanda ake zargi da aikata laifukan yaƙi, yana mai cewa ya kamata ya gurfana a gaban kotun da ke Hague.
Sai dai gwamnatin Isra’ila ta musanta zarge-zargen, tana mai cewa hare-haren da ta kai a Gaza sun dace da dokokin ƙasa da ƙasa, yayin da Netanyahu ya ce sammacin kama shi yana da dalilan siyasa.
A gefe guda kuma, Amurka ba mamba ba ce ta ICC, don haka ba ta da wajibcin aiwatar da sammacin kama da kotun ke bayarwa. Jami’an gwamnatin Amurka sun kuma soki kalaman Mamdani, suna mai cewa ba su amince da ikon ICC ba.
Duk da cece-kucen, jakadan Isra’ila a Majalisar Ɗinkin Duniya, Danny Danon, ya tabbatar da cewa Netanyahu zai halarci taron UNGA kamar yadda aka tsara, inda zai gabatar da jawabi kan matsayar Isra’ila.
