Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Gwamnatin Jihar Katsina ta horas da jami’an gwamnati kan inganta aiwatar da Shirin HOPE na Bankin Duniya.
Hukumar kula da tsare-tsaren cigaban Jihar Katsina (KTDMB) ta shirya wani kwas na kwanaki biyu domin horas da manyan jami’an gwamnati kan yadda za a inganta aiwatar da shirin Bankin Duniya na HOPE.
HOPE na Bankin Duniya yana da manufar inganta yadda ake tafiyar da ayyukan gwamnati da kuma samar da cigaba ga al’umma.
Shirin yana da ginshiƙai guda 3 da suka hada da ɓangaren tafiyar da gwamnati watau HOPE-Gov, ɓangaren inganta harkar ilimi watau HOPE-Edu da kuma ɓangaren inganta harkar lafiya, watau HOPE-PHC a jihar.
Horon ya tattaro manyan jami’ai daga ɓangarorin ilimi, kiwon lafiya da harkokin mulki, ciki har da kwamishinoni, shugabannin hukumomi, jami’an gwamnati da masu kula da shirin.
A yayin bayar da horon, an mayar da hankali ne wajen inganta haɗin gwiwa a tsakanin dukkan ɓangarorin da tabbatar da cewa jihar ta samu cimma kyakkyawan sakamako a ƙarƙashin shirin a dukkan ɓangarori guda uku, waɗanda suka shafi inganta tsarin mulki, samar da ingantaccen kiwon lafiya na matakin farko da kuma bunƙasa harkar ilimi.
A yayin horon, mahalarta sun duba matakin shirye-shiryen jihar, tare da gano muhimman abubuwan da ya kamata a bai wa fifiko a sassa daban-daban. Haka kuma, sun tsara tsarin aiki na bai ɗaya da zai jagoranci aiwatar da shirye-shiryen.
Mahalarta taron sun kuma amince da buƙatar ƙara haɗin gwiwa tsakanin ma’aikatu, hukumomi da sauran sassan gwamnati domin tabbatar da ingantaccen aiwatar da shirye-shiryen da kuma bibiyar ci gaban da ake samu.
Ana sa ran horon zai taimaka wajen inganta shirin da Katsina ke yi na shekarar kuɗi ta 2027, tare da bai wa jihar damar cin gajiyar fa’idodi da sakamakon da ake samu ƙarƙashin shirye-shiryen HOPE.
