Mashaƙo: Nijeriya na fuskantar barazanar cuta duk da samuwar rigakafi

Spread the love

Rufe giɓin cutar mashaƙo, wato diphtheria a Nijeriya ya zama abin damuwa, duk da cewa akwai ingantaccen allurar rigakafin cutar da aka tabbatar da amincinta. Yawaitar ɓullar cutar a sassa daban-daban na ƙasar na buƙatar ɗaukar matakin gaggawa da kuma haɗin gwiwar gwamnati a dukkan matakai.

Hukumar Daƙile da Kula da Cututtuka Masu Yaɗuwa ta Nijeriya (NCDC) ta ce an tabbatar da sama da mutane 10,000 da suka kamu da cutar mashaƙo a bana, inda jihohin Arewa da Tsakiyar Nijeriya, ciki har da Kano, Katsina, Bauchi da Filato, ke cikin jihohin da cutar ta fi ƙamari.

Haka kuma, an samu rahoton mutuwar sama da mutane 300 sakamakon cutar.

Ko da yake adadin waɗanda ke mutuwa daga cikin waɗanda aka tabbatar sun kamu da cutar ya ragu sosai idan aka kwatanta da makamancin lokacin bara, NCDC ta yi gargaɗin cewa ci gaba da samun masu fama da cutar na ci gaba da zama babbar barazana ga lafiyar jama’a.

A cewar Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO), diphtheria cuta ce da ƙwayoyin cuta ke haddasawa, wadda galibi ke shafar sassan maƙogwaro da hanyoyin numfashi na sama, kuma a wasu lokutan tana iya bayyana a fata.

ƙwayar cutar tana samar da wani guba da zai iya lalata muhimman gaɓoɓin jiki, musamman zuciya da jijiyoyin ƙwaƙwalwa, lamarin da ke sanya cutar cikin waɗanda ka iya yin barazana ga rayuwa.

Abin da ya fi tayar da hankali game da ci gaba da ɓullar diphtheria shi ne cewa cuta ce da za a iya hana kamuwarta ta hanyar allurar rigakafi.

Sai dai samun cikakkiyar kariya na buƙatar yin allurai da dama, tare da ƙarin allurar ƙarfafa garkuwar jiki domin tabbatar da kuma ɗorewar kariya daga cutar.

WHO ta kiyasta cewa a shekarar 2025, kusan kashi 85 cikin 100 na jarirai a faɗin duniya, wato kimanin yara miliyan 110, sun samu allurai uku da ake ba da shawarar a yi na rigakafin diphtheria.

Wannan na nufin kusan kashi 15 cikin 100, ko kuma kusan jarirai miliyan 20, ba su samu cikakkiyar kariya ba ko kuma ba su samu allurar kwata-kwata ba.

Bambancin da ake samu wajen yawan mutanen da ke samun allurar rigakafi tsakanin ƙasashe da ma cikin ƙasa ɗaya, na ci gaba da zama babban ƙalubale.

WHO ta ce, ƙasashe 83 ne kawai suka shigar da dukkan allurai ukun na ƙarfafa garkuwar jiki da ake ba da shawarar yi kan diphtheria cikin shirye-shiryen rigakafinsu na ƙasa, yayin da ƙasashe 42 kuma ba su da ko da ɗaya daga cikin waɗannan ƙarin allurai.

Sabbin ɓarkewar cutar na ƙara nuna muhimmancin ci gaba da samun yawan mutanen da suka samu cikakkiyar rigakafi, ba tsakanin jarirai kaɗai ba, har ma da yara da matasa.

Mutanen da ba su samu allurar ba ko kuma ba su kammala yawan alluran da ake buƙata ba, su ne suka fi fuskantar haɗarin kamuwa da cutar.

Idan ba a samu kulawar da ta dace ba, diphtheria na iya yin sanadin mutuwar kusan kashi 30 cikin 100 na masu kamuwa da ita, yayin da ƙananan yara ke fuskantar haɗarin mutuwa fiye da sauran.

Nijeriya, wadda ta sha fuskantar ɓarkewar wannan cuta, ba za ta iya ci gaba da ɗaukar diphtheria a matsayin wata matsala da ake tunkararta ne kawai idan ta barke ba.

Wani bincike da aka wallafa ta hanyar ScienceDirect ya nuna cewa a ƙasashe masu ƙarancin kuɗin shiga da matsakaicin kuɗin shiga, irin su Nijeriya, abubuwan da ke taimakawa wajen ɓarkewar diphtheria sun haɗa da ƙarancin samun allurar rigakafi, rashin bin tsarin rigakafin yara yadda ya kamata, wasu shingayen al’adu da addini, jinkirin amincewa da allura, yaɗuwar bayanan ƙarya, raunin tsarin kiwon lafiya da kuma rashin kyawun yanayin rayuwa.

Rashin tsaro, kaura da tarwatsewar al’umma, yawan zirga-zirgar jama’a da kuma iyakokin ƙasa da ba su da cikakken tsaro, duk suna ƙara dagula lamarin, saboda suna iya taimakawa wajen yaɗuwar cututtuka masu yaɗuwa.

Haka kuma, saurin ƙaruwa da yawan jama’a da taɓarɓarewar muhalli, musamman ƙarancin ruwa wanda ke kawo cikas ga tsafta da muhalli, na iya ƙara jefa al’ummomi cikin haɗarin kamuwa da cutar.

Abin lura shi ne cewa ana zargin sama da kashi 60 cikin 100 na mutanen da ake zargin sun kamu da diphtheria a Nijeriya ba su samu allurar rigakafin cutar ba. Wannan na nuna ƙarara cewa ƙarancin yawan mutanen da aka yi wa rigakafi na daga cikin manyan abubuwan da ke haddasa ci gaba da ɓarkewar cutar.

Darakta-Janar na NCDC, Dakta Jide Idris, ya bayyana ƙarancin yawan mutanen da aka yi wa rigakafi, musamman rashin samun allura ta uku ta rigakafin diphtheria, a matsayin ɗaya daga cikin manyan abubuwan da ke taimakawa wajen yaɗuwar cutar.

Yara da dama har yanzu ba su samu ko allura ɗaya ba, yayin da wasu kuma ba su kammala alluran da ake buƙata ba.

Jinkirin amincewa da allurar rigakafi, rashin tsaro, wahalar isa ga wasu al’ummomi, kaura da yawan motsin jama’a, duk sun kawo cikas wajen kai rigakafin ga kowane yaro da ke buƙatar kariya.

A gefe guda kuma, cunkoson da ke akwai a cibiyoyin kiwon lafiya da ƙarancin maganin guba na diphtheria, wato diphtheria antitoɗin, na iya jinkirta fara jinya tare da ƙara haɗarin samun matsaloli ko mutuwa.

Sauran abubuwan da ke taimakawa wajen yaɗuwar cutar sun haɗa da rashin tsaftar muhalli, ƙarancin samun muhimman ayyukan kiwon lafiya da kuma ƙarancin binciken likitanci da na annoba da zai taimaka wajen gano cutar da wuri da kuma samar da ingantaccen matakin daƙile ta.

A ganinmu, daƙile yaɗuwar diphtheria na buƙatar a sauya salo daga dogaro da tunkarar ɓarkewar cuta bayan ta faru, zuwa tsarin rigakafi da kariya na dindindin.

Abu na farko da ya kamata a bai wa fifiko shi ne rufe giɓin da ke akwai wajen yin rigakafi, tare da tabbatar da cewa an kai ga kowane yaro da ya cancanci allura amma ya rasa wata daga cikin alluran da ake buƙata.

Ya kamata a ƙarfafa tsarin rigakafin yau da kullum da sa ido kan cututtuka ta hanyar cibiyoyin kiwon lafiya na matakin farko.

Kowane yaro ya kamata ya samu allurai uku na farko na rigakafin diphtheria a lokacin jarirai, sannan ya samu ƙarin alluran ƙarfafa garkuwar jiki a lokacin ƙuruciya da samartaka, bisa tsarin da ya dace.

Ya kamata gwamnatoci su gaggauta gano al’ummomin da ke da ƙarancin yawan masu samun rigakafi, tare da tura tawagogin yin allurar rigakafi masu zirga-zirga zuwa ƙauyuka da sauran wuraren da ake buƙata.

Ya kamata a ba da kulawa ta musamman ga yara da ke cikin al’ummomin da ba sa samun isassun ayyukan kiwon lafiya, waɗanda suka rasa matsugunansu ko kuma waɗanda ke zaune a wuraren da ke da wahalar isa.

Haka kuma, akwai buƙatar ƙara haɗin gwiwa tsakanin Gwamnatin Tarayya, gwamnatocin jihohi da ƙananan hukumomi, cibiyoyin kiwon lafiya, sarakunan gargajiya da shugabannin addinai, ƙungiyoyin al’umma da abokan hulɗar ci gaba.

Ya kamata a ƙarfafa tsarin sa ido kan cututtuka da ƙarfin ɗakunan gwaje-gwaje, yayin da ma’aikatan kiwon lafiya ke buƙatar isasshen tallafi wajen gano cutar, kula da marasa lafiya da kuma ɗaukar matakan kariya daga yaɗuwar cututtuka.

Muna goyon bayan kiran NCDC ga gwamnatocin jihohi da ƙananan hukumomi da su ƙara ƙaimi wajen mayar da martani, ta hanyar gano al’ummomin da suka fi fuskantar haɗarin cutar da kuma karkatar da ma’aikata, kayan aiki da kuɗaɗen da ake da su zuwa wuraren da gibin kariya ya fi tsanani.

Shigar Gwamnatin Tarayya kaɗai ba zai wadatar wajen kawo ƙarshen ɓarkewar cutar ba. Dole ne matakan yaƙi da cutar su isa matakin jiha, ƙaramar hukuma, cibiyar kiwon lafiya da kuma al’umma.

A ƙarshe, al’ummar Nijeriya ma na da rawar da za su taka wajen daƙile cutar. Ya kamata a tabbatar da cewa ruwan sha yana da tsafta, a kiyaye tsabtar muhalli, a yi amfani da ingantattun wuraren bayan gida, a guji yin bahaya a fili, sannan a riƙa wanke hannu akai-akai da sabulu da ruwa mai tsafta.

Haka kuma, ya kamata a tabbatar an dafa abinci yadda ya kamata, an adana shi cikin yanayin da ya dace, kuma an kare shi daga gurɓacewa.

Bai kamata diphtheria ta ci gaba da salwantar da rayukan ’yan Nijeriya ba alhali akwai ingantacciyar hanyar kare kai daga cutar.

Barkewar cutar da ake fuskanta a yanzu ya kamata ta zama babban kira ga gwamnati da al’umma baki ɗaya da su farka daga barci.

Nijeriya na buƙatar rufe giɓin da ke akwai wajen yin rigakafi, ƙarfafa tsarin kiwon lafiyarta, tare da tabbatar da cewa babu wani yaro da aka bari ba tare da kariya daga wannan cuta ba.

By ukarofi

Leave a Reply