A yau, Nijeriya na tsaye a wani wuri mai rikitarwa tsakanin sani da kuma sakaci. Duk da yawan bayanai, bincike da kuma gargaɗin masana kiwon lafiya, cutar sikila na ci gaba da yaɗuwa cikin al’umma, tana jefa dubban iyalai cikin wahala da damuwa. Wannan yanayi ya nuna cewa matsalar ba wai rashin sani ba ne kawai, har ma da gazawar aiwatar da abin da aka sani.
Cutar sikila cuta ce ta gado da ke shafar ƙwayoyin jini, musamman “Red Blood Cells” (RBC), waɗanda ke ɗauke da sinadarin haemoglobin. Idan wannan haemoglobin ya samu matsala, ƙwayoyin jini kan sauya siffa, su zama kamar sikila, wanda ke hana su yin aikinsu yadda ya kamata. Wannan ne ke haddasa yawan ciwo, rauni da sauran matsaloli ga masu fama da cutar.
Abin da ya fi tayar da hankali shi ne cewa wannan cuta na daga cikin cututtukan da za a iya kaucewa kafin samuwarta. Ta hanyar gwajin genotype kafin aure, ana iya tabbatar da cewa ma’aurata ba za su haifi ’ya’ya masu ɗauke da cutar ba. Amma duk da wannan sauƙi, har yanzu mutane da dama suna yin watsi da wannan shawara.
A ƙasar nan, an riga an tabbatar da cewa Nijeriya na daga cikin ƙasashen da ke da mafi yawan masu cutar sikila a duniya. A kowace shekara, ana haihuwar dubban jarirai da wannan cuta, kuma da yawa daga cikinsu ba sa kaiwa ga balaga. Wannan ba wai kawai asarar rayuka ba ne, har ma da asarar ƙarfi da ci gaban al’umma.
Abin tambaya a nan shi ne: me ya sa wannan matsala ke ci gaba da ƙaruwa duk da cewa an san hanyoyin magance ta?
Na farko, akwai matsalar wayar da kai. A yankunan karkara da dama, mutane ba su da cikakken ilimi kan cutar sikila. Wasu ma ba su san ma’anar genotype ba, balle su fahimci muhimmancin gwaji kafin aure. Wannan giɓi na ilimi na haifar da yanke shawara ba bisa ƙa’ida ba, wanda ke jefa sabbin ƙarni cikin wahala.
Na biyu, akwai al’ada da imani da ke sa mutane su yi watsi da shawarwarin likitoci. Wasu ma’aurata, ko da sun san cewa su duka suna da rukunin jini marasa dacewa, suna tafiya su yi aure da fatan cewa addini ko ƙaddara za su sauya sakamakon. Amma gaskiya ita ce, ƙwayoyin halitta ba sa canjawa da fata kawai.
Na uku, akwai matsalar tsarin kiwon lafiya. Duk da cewa akwai wasu ƙoƙari na bincike da ƙirƙire-ƙirƙire a ƙasar, yawanci ba sa samun ci gaba zuwa matakin da za su amfani jama’a baki ɗaya. A lokuta da dama, ana fara bincike mai kyau, amma daga baya a watsar da shi sakamakon rashin kuɗi ko rashin tsari mai ɗorewa.
Masu fama da cutar sikila na rayuwa cikin wahala mai tsanani. Suna fuskantar yawan rashin lafiya, ciwon ƙashi, ƙarancin jini, da kuma barazanar mutuwa tun suna ƙanana. Iyaye kuma na fama da nauyin kuɗin jinya da damuwar rashin tabbas kan makomar ’ya’yansu. Wannan ba kawai matsalar lafiya ba ce, matsala ce ta zamantakewa da tattalin arziki.
Duk da haka, akwai hanyoyi masu sauƙi da za a iya bi domin rage wannan matsala.
Abu na farko shi ne sanya gwajin jini kafin aure ya zama wajibi. Wannan ya kamata ya zama doka, ba shawara kawai ba. Duk wanda zai yi aure ya kamata ya gabatar da sakamakon gwajin genotype, domin kare lafiyar al’umma gaba ɗaya.
Na biyu, ya zama dole gwamnati ta fara gwajin jarirai tun daga haihuwa. Idan aka gano cutar da wuri, ana iya ba da magunguna da kulawa da za su taimaka wajen tsawaita rayuwa da rage wahala.
Na uku, ya zama wajibi a samar da magunguna masu sauƙin samu da rahusa. Magunguna kamar folic acid, penicillin, da hydroɗyurea suna da matuƙar muhimmanci wajen rage tsanani da yawan tashin cutar. Amma da yawa daga cikin marasa lafiya ba sa samun su yadda ya kamata.
Haka kuma, ya kamata a kafa cibiyoyin dashen ɓargo (bone marrow transplant) a sassa daban-daban na ƙasar. Duk da cewa wannan hanya tana da tsada kuma ba koyaushe take samun nasara ba, ita ce hanya mafi kusa da warkar da cutar gaba ɗaya.
Bugu da ƙari, ya zama dole a ƙarfafa bincike da ƙirƙire-ƙirƙire a fannin lafiya. Nijeriya na da ƙwararrun masana da za su iya samar da hanyoyin magani, amma suna buƙatar goyon bayan gwamnati da masu zaman kansu domin ganin aikinsu ya zama mai amfani ga jama’a.
Wayar da kai ma na da matuƙar muhimmanci. Dole ne a shiga makarantu, masallatai, coci-coci da sauran wuraren taro domin ilmantar da jama’a kan illar cutar sikila da hanyoyin kauce mata. Ba za a iya daƙile wannan matsala ba tare da haɗin kan al’umma gaba ɗaya ba.
A ƙarshe, ya zama dole mu fahimci cewa cutar sikila ba wata matsala ce da ba za a iya shawo kanta ba. Hanyoyin magance ta a bayyane suke: gwaji kafin aure, ilimi, kulawa mai kyau, da kuma tsari mai ɗorewa daga gwamnati.
Idan muka ci gaba da yin sakaci, za mu ci gaba da haifar da sabbin ƙarni da ke fuskantar wahala da za a iya kaucewa. Amma idan muka ɗauki mataki a yau, za mu iya rage yawan masu cutar, mu kuma inganta rayuwar waɗanda ke fama da ita.
Lokaci ya yi da Nijeriya za ta daina kallon cutar sikila a matsayin wata matsala ta yau da kullum, ta mai da ita babban abin da ya kamata a ba fifiko. Wannan ya shafi rayuka, makoma, da ci gaban ƙasa baki ɗaya.
