A shirye muke mu janye yajin aiki – ASUU

…Amma idan an cimma matsaya, inji shugabanta
*Ya ce, shigar da ƙungiyar ƙara ba mafita ba ce
*Za mu cigaba da shiga tsakani don kawo ƙarshe, cewar wata ƙungiya

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Sama da watanni bakwai kenan Ƙungiyar Malaman Jami’o’i a Nijeriya (ASUU) na cigaba da yajin aiki akan wasu buƙatu da suke neman gwamnati ta cika.

Duk da zaman tattaunawa da ƙungiyar ta riƙa yi da Gwamnatin Tarayya akai-akai don sasantawa, amma ba a cimma wata matsaya ba, lamarin da ya haifar da kowanne vangare na zargin juna da nuna son zuciya, inda a gefe guda kuma ɗalibai na tsala kuka sakamakon zaman jiran da suke ta yi a gidajensu na hutun dole.

To sai da kuma, a jiya Alhamis, Shugaban Ƙungiyar ASUU na Ƙasa, Farfesa Emmanuel Osodeke, da kansa ya ce, ƙungiyar na son kawo ƙarshen yajin aikin, amma ya yi togaciya da cewa, idan an cimma yarjejeniya ta zahiri da Gwamnatin Tarayya.

Mista Osodeke ya bayar da wannan tabbacin ne a Abuja a wani taro na ƙasa da ƙasa kan ilimin manyan makarantu da yadda za a bunƙasa harkar ilimi a ƙasar.

Idan za a iya tunawa, ƙungiyar ta fara yajin aiki ne a ranar 14 ga Fabrairu, wanda hakan ya sa ta shafe watanni bakwai da rufe jami’o’in gwamnati a faɗin ƙasar, duk da za a iya cewa, yajin aikin ya wuce hakan ma, domin a wajejen watan Nuwanba na 2021 ta fara tafiya yajin aikin gargaɗi.

A kwanakin baya ne Gwamnatin Tarayya ta maka Ƙungiyar ASUU ƙara a Kotun Masana’antu da nufin kawo ƙarshen yajin aikin bayan da lamarin sasantawa ke cigaba da cin tura.

“Akan dukkan waɗannan batutuwa, mun bai wa gwamnati mafi ƙarancin abin da za mu iya karɓa, amma ba su mayar da martani kan batun sake farfaɗo da su ba, kan batun alawus-alawus da ake samu da kuma batutuwan da muka tattauna.

“Mun yi shawarwari kuma mun amince da su sanya hannu, kuma wannan abu ne mai sauqi, ba fiye da kwana ɗaya ba.

“Akan UTAS da IPPIS, sai mu ce ku fitar da rahoton gwajin da kuka yi, mu duba wanda ya zo na farko mai dama-dama mu ɗauka kamar yadda muka amince.

“Don haka mun ba su mafi ƙarancin abin da muke so kuma dole ne mu sauko, kuma za su iya yin hakan a rana ɗaya idan ana so,” inji shi.

Don haka Mista Osodeke, ya nanata ƙudirin ƙungiyar na komawa makaranta idan Gwamnatin Tarayya ta ɗora ƙudirinta a kan teburi, yana mai cewa za a iya cimma matsaya idan gwamnati ta so.

“Idan har gwamnati na son ƙasar nan, yaran nan da iyayensu, to su hau kan teburi mu warware waɗannan matsaloli a rana guda.

“Kamar yadda muka yi a shekarar 2014, su zo su tabbatar mun yi hakan, mu ma za mu iya yin taron a fili domin Nijeriya ta ga abin da muke tattaunawa,” inji shi.

Shugaban ASUU ya bayyana baqin cikinsa kan yajin aikin da har Gwamnatin Tarayua za ta kai ƙungiyar kotu.

Ya ce shigar da ƙungiyar ƙara ba abu ne da ya dace ba, domin a cewarsa hakan zai qara dagula al’amuran ɗalibai da manyan makarantun ƙasar nan.

Ya ce idan har kotu ta tilasta wa malaman makarantar su koma makaranta, ba za su tilasta musu koyarwa da idon basira ba, inda ya ce ko shakka babu ɗaliban za su yi karatu.

Mista Osodeke ya yaba wa Kwamitin Mataimakan Shugaban Ƙasa da masu goyon bayan waɗanda suka shiga don warware matsalolin.

Don haka ya yi kira ga iyaye da ɗalibai da su yi kira ga gwamnati da ta yi abin da ya kamata domin yajin aikin ya zo ƙarshe ba tare da cin mutunci ko aibanta ƙungiyar ba.

A halin da ake ciki kuma, Vivian Bello, wata mai fafutika akan harkar ilimi a Save Public Education Campaign, wata ƙungiya mai zaman kanta, ta roƙi ɓangarorin biyu da su warware matsalolin, inda ta ce ba ɗaliban ne kaɗai ke jin zafin wannan dogon yajin aikin ba, har ma da ƙungiyar.

Misis Bello ta ce ya kamata ɓangarorin biyu su kawo ƙarshen rikicin domin kare ɗalibai da kuma ci gaban ilimi a ƙasar nan.

“Za mu taka rawarmu ta gargajiya, wacce ita ce aikin sa ido. Za mu cigaba da bin diddigin ɓangarorin biyu, wato na Gwamnatin Tarayya da kuma Ƙungiyar ASUU, domin ganin an kawo ƙarshen wannan batu na kai da kawowa cikin gaggawa za a janye yajin aikin,” inji ta.

Wasu daga cikin batutuwan da suka haifar da yajin aikin da ƙungiyoyin suka haɗa da rashin sakin asusun farfaɗo da tattalin arziki, rashin biyan alawus-alawus ɗin da aka samu (ko kuɗaɗen alawus na ilimi), sake tattaunawa kan yarjejeniyar 2009, da fitar da farar takarda ga ƙungiyar.

Sauran buƙatun sun haɗa da rashin biyan mafi ƙarancin albashi da kuma rashin daidaito da ake samu ta hanyar amfani da ‘Integrated Payroll and Personnel Information System’ (wato IPPIS a taƙaice).

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *