Wayar salula ta taimaka wajen samar da sana’o’i ga matasa – Ashiru Yakasai

Daga IBRAHIM MUHAMMAD a Kano

An bayyana shigowar wayar hannu na tafi da gidanka a ƙasar nan ya taimaka sosai wajen samar wa ɗimbin matasa aikin yi da kuma haɓaka tattalin arziki.

Jami’n hulɗa da jama’a na ƙungiyar kasuwar waya na titin Bairut kuma wanda shine jimi’in hulɗa da jama’a na biyu na ƙungiyar ‘yan waya na Jihar Kano AMPAT, Ashiru Yusuf Yakasai shine ya bayyana hakan.

Ya ce zuwan wayar hannu ya sauƙaƙa gudanar da harkokin kasuwanci ta yadda ake iya yin amfani da wayar wajen ƙulla hulɗa ta kasuwanci cikin sauƙi daga zaune za ka iya sayen duk abinda kake da buƙata.

Ya ce mutane da yawa a jihar nan a dalillin waya sun samu arziƙi kuma wayar ta samawa matasa madogara ta hana zaman banza domin kusan matasa sune kan gaba a harkar saye da sayarwar waya.

Ashiru Yusuf ya ce a harkar waya ne sai ka samu ɗan ƙaramin shago da ake hada-hadar waya ka samu akwai yara sama da 10 a ƙarƙashinsa.

Shugaban na kamfanin wayoyi na Goma Phone, Ashiru Yusuf ya ce yanzu waya ta zama abokiyar rayuwa mafi yawan jama’a na amfani da ita kuma duk inda ka shiga za ka samu akwai masu sana’ar saye da sayarwar wayar.

Ya ce wannan ta sa ake samun ƙalubale ta ɓangarori daban-daban amma ƙungiyarsu da haɗin gwiwar jami’an tsaro na ɗaukar matakai na kauda ɓata gari dake shigowa cikinsu.

Ashiru Yusuf Yakasai ya ce a baya wani shugaba a ƙasar nan ya taɓa cewa mai arziƙi da masu ƙaramin ƙarfi sai an zo lokacin da kusan kowa sai ya mallaki waya kuma maganar ta sa yanzu ta tabbata.

Jami’in hulɗa da jama’a na ƙungiyar masu waya na AMPAT, Ashiru Yakasai ya yi kira ga matasa da suke harkar waya su kasance masu gaskiya da amana a harkokinsu kuma su guji yin hulɗa da ɓatagari.

Yakasai ya kuma ce ƙungiyarsu tana ɗaukar matakai don kauda duk wani baragurbi da zai fake da sana’arsu don cutar da mutane.