Abduljabbar ya ƙalubalanci hukuncin kisa da kotu ta yanke masa

Daga Ibrahim Hamisu, Kano

Malam Abduljabbar Nasir Kabara wanda Kotu ta zartar wa da hukuncin kisa ta hanyar rataya ya ce bai gamsu da hukuncin da aka yi masa ba gaba ɗaya.

Wannan na ƙunshe ne cikin wata takarda da lauyansa ya miƙa wa Babbar Kotun Jihar Kano.

Cikin takardar, ya ce “Ni Abduljabbar ban gamsu da hukuncin da Kotun Shari’ar Musulunci ta Ƙofar Kudu ta yanke a kaina ba, a shari’a mai lamba CR/01/2021 da aka zartar ranar 15th Disamba, 2022, ƙarƙashin Alƙali Ibrahim Sarki Yola.”

Abduljabbar ya ɗaukaka ƙara zuwa Babbar Kotun jihar Kano bisa dalilin da ya bayyana a sakin layi na 3 na takardar ɗaukaka ƙarar.

Cikin takardar ya ce bai yarda da dukkan hukuncin da kkaramar kotun ta yanke masa ba.

Ya kuma buƙaci Kotun Ɗaukaka Ƙara da ta yi la’akari da duk buƙatun da ya bayyana a sakin layi na huɗu na wannan takardan ɗaukaka ƙara.

Malam Abduljabbar ɗin ya cigaba da bayyana cewa ya bayyana sunayen duk waɗanda wannan roƙo ya shafa kai tsaye a sakin layi na biya na takardan ɗaukaka ƙara.

Kazalika, ya bayyana cewa hukuncin da aka yi masa ya saɓa da tanadin da dokar Shari’a ta shekara ta 2000 ta Jihar Kano ta yi.

Ita dai Kotun Shari’ar Muslunci da ke Ƙofar Kudu ta bai wa malam Abduljabbar da gwamnatin Kano kwanaki 30 daga 15/12/22 domin ɗaukaka ƙara ga wanda bai gamsu da hukuncin nata ba.