Yadda karatun jami’a ke neman zama ƙwalele ga talakan Nijeriya

Daga HARUNA UMAR JOS

Ga dukkan alamu, shekarar 2022 ita ce shekarar ƙarshe da yaron talaka a Nijeriya zai tafi ƙaro karatu a jami’a (University), ganin yadda wasu takardu masu alaqa da wasu daga cikin jami’oin ke nuna yadda ake shirin ninka kuɗin makaranta, ko ma dai na ce an ninka!

Ta iya yiwuwa wannan lamari yana da alaƙa da artabun da ke tsakanin gwamnati da malaman jami’o’i. Ko ma dai menene, da gwamnati da ku malamai, ku tuna fa wannan dambarwa taku a kan ‘ya’yan talakawa take ƙarewa. Tana ƙarewa ne a kan mutanen da suke neman na sa wa a baka, kafin ma komai.

A ranar 14 ga watan Fabrairun 2022, ƙungiyar malaman jami’o’i ta ƙasa, ASUU, ta shiga yajin aikin gargaɗi bayan ta zargi gwamnatin Najeriya da ƙin cika mata alƙawuran da ta ɗauka. Bayan tsahon lokaci, wannan lamari ya sanya ƙungiyar ta yi ta zama da wakilan gwamnati. Wani lokaci a rabu ‘baran-baran’, wani lokaci kuma a rabu ana yaƙe (murmushin da bai kai har zuci ba).

Shigar ƙungiyar ASUU yajin aiki ya sanya gwamnatin tarayya a ƙarƙashin jagorancin shugaba Muhammadu Buhari ƙin biyan malaman jami’o’i kuɗaɗensu. Dalili kuwa shi ne tabbatuwar tsarin nan na “NO WORK NO VOTE”, ma’ana, babu biya idan ba a yi aiki ba. Wannan mataki ya sanya ƙungiyar ASUU ci gaba da zaman gida har sai da ‘ya’yan ƙungiyar suka kwashe watanni bakwai a zaune, lamarin da wasu ke ganin ya yi sanadiyar mutuwar wasu daga cikin malaman jami’o’i, wasu kuma sun shiga halin matsi.

Bayan cikar ƙungiyar ASUU watanni bakwai tana yajin aiki, kakakin majalisar wakilai, Honourable Femi Gbajabiamila (mai ritaya), ya yi nasarar sasanta ɓangarorin biyu, lamarin da ya sanya shi yin fice a faɗin Najeriya, la’akari da cewa waɗanda abin ya shafa, kamar ministan ilimi, Malam Adamu Adamu da ministan ayyuka da ɗaukar ma’aikata, dakta Chris Ngige sun gaza shawo kan lamarin.

Daga ƙarshe dai ASUU ta janye yajin aikin na wucin gadi a ranar 14 ga watan Oktoban 2022, bayan wata 8 dai-dai kenan da shigar ta yajin aikin. Allah Ya saka wa Honourable Femi Gbajabiamila (mai ritaya) da alkhairi a bisa jajircewar da ya yi na sasanci tsakanin ASUU da Gwamnatin Tarayya. Wannan a ɓangaren gwamnati da malamai kenan.

Idan na dawo ɓangaren ɗalibai kuma, tsawon lokacin da suka kwashe a gida sun yi hutu ne cikin fargaba da tunanin cewa a kowanne lokaci za su iya komawa makaranta. Wannan tunani ya sanya da dama daga cikin ɗalibai ƙin kama sana’o’i saboda suna gudun kar su fara aiki kuma ASUU ta janye yajin aiki.

Mai karatu zai iya cewa “to ai wannan ba shi ne karon farko da ASUU ta tafi yajin aiki ba”, to amma duk da haka, kowanne yajin aiki da yadda ya ke kasancewa.

Yajin aikin ASUU ya shafi ɗaliban jami’o’i fiye da duk wani mai ruwa da tsaki a harkar ilimi! Ɗalibin da ya kamata a ce ya kammala karatunsa na digiri a shekaru huɗu ba ya samun damar hakan. Sai ka ga a maimakon shekaru huɗu, mutum ya kwashe shekaru shida ko fiye da hakan (ya danganta da yanayi na cin jarabawa ko akasin haka).

Bayan ƙarin wa’adin karatu, ɗalibai da dama da suke da burin mallakar shaidar kammala jami’a sun haɗu da ajalinsu. Wasu sun mutu a sanadiyar baqin cikin yajin aiki, wasu kuma sun mutu a sanadiyar neman na jefawa a baki tunda dai ba makaranta (duk da cewa kowa ba ya wuce ajalin sa).

Masu raunanan zuciya sun yi amfani da rauninsu wajen kwashe wa ɗalibai kayayyaki da suka bari a ɗakunan kwanan ɗalibai kafin su tafi yajin aikin da ba su da damar sa wa a yi ko su hana. Allah Sarki, ɗalibi bawan Allah! Idan za ka tashi hankali sai a ce kai mai ilimi ne. Allah Ya yi wa iliminka albarka. Amin.

Bayan dukkan waɗannan ƙalubale da ɗalibai suka fuskanta, sai ga shi a kwanakin nan wasu daga cikin manyan jami’o’in ƙasar nan sun fara fitar da sabbin tsare-tsaren biyan kuɗi. Wasu makarantu sun ƙara kaso kaɗan, yayin da wasu kuma suka ninka kuɗin da hankali ma ba zai ɗauka ba.

Wannan lamari ya tayar da hankalin duk wani ɗalibi, musamman ma wanda ya fito daga gidan da ba su da ƙarfi. Da yawa daga cikin ɗalibai sun shiga fargaba, inda wasu da dama ke tunanin ko da akwai yiwuwar su ciga da karatu ko kuma su haƙura, su ajiye. Allah Ya tausaya wa bayi.

Wannan dalili ya sanya ni zanta wa da wasu al’umma da suka haɗa da ɗalibai da masu riqe da ragamar gida, inda suka tabbatar min da halin da suke ciki.

“Wata rana muna zaune bayan an gama darasi, wani daga cikin malamanmu ya kunna wayarsa, sai ya nuna mana sabon jadawalin kuɗin makaranta da za mu riƙa biya nan gaba kaɗan,” cewar wani ɗalibi da ya fito daga ɗaya daga cikin jami’oin gwamnatin tarayya a shiyyar Arewa maso Gabas.

“Ni nake ɗaukar nauyin karatun ƙannena. Zan sa ƙanina ƙwaya ɗaya a sabuwar makarantar koyon aikin likitanci da aka buɗe a ƙaramar hukumarmu, amma abin ya fi ƙarfina. Yanzu mun haƙura,” cewar wani yaya da ya yi ƙoƙarin kai ƙaninsa jami’a.

Shi kuwa wani uba cewa ya yi: “Na yi burin na kai ‘ya ta makarantar gaba da sakandiri, to amma na ga abin ba mai yiwuwa ba ne. Yanzu na bar wa Allah komai. Ina addu’ar Allah Ya ba ni yadda zan yi na aurar da ita kawai.”

Yanzu dai shekarar 2022 ta zo ƙarshe. Al’ummar duniya na shirye-shiryen shiga sabuwar shekara ta 2023. Al’ummar Najeriya, musamman ɗalibai na fargabar shiga sabuwar shekarar, kasancewar ba su san da wanne salo shekarar za ta zo musu ba. Shin akwai yiwuwar ASUU ta ƙara shiga yajin aiki? Shin dukkan jami’o’i za su huce haushinsu ne ta hanyar qara wa ɗalibai kuƙin makaranta?

Ko dai wani dalili zai zo da zai sa waɗannan matsaloli ba za a sake fuskantarsu ba? Koma dai menene, fatanmu shi ne, Allah Ya sa daga shekarar 2022 matsalolin da suke addabar fannin ilimi sun zo ƙarshe. Allah Ya sa ɗalibai za su samu damar sararawa a sabuwar shekarar da za a shiga. Allah Ya zaunar da kowa lafiya a Naijeriya da duniya bakiɗaya. Allah Ya sa a gudanar da zaɓukan Najeriya lafiya, Ya kuma bai wa Nijeriya shuwagabanni na gari.

Da ga ƙarshe, Ina mai amfani da wannan dama wajen yin kira ga shugaban ƙasa mai shirin barin gado, Muhammadu Buhari; da shugaban ƙasa mai rabo a babban zaɓen shekarar 2023, da ministocin da abin ya shafa masu ci, ministocin da abin ya shafa masu zuwa, da dukkan ‘yan majalisu, hukumomin kula da karatu a dukkan matakai, hukumar kula da karatun jami’a, shuwagabannin jami’o’i da malaman su, da sauran masu ruwa da tsaki a harkar ilimi, a ji koken talakawa, a taimaki fannin ilimi, kana a yi duba a kan batun ƙara wa ɗalibai kuɗaɗen makaranta, domin hakan zai iya sanadin ajiye karatun da yawa daga cikin ɗalibai.

Haruna Umar ɗan ƙasa ne mai bayyana ra’ayi. Ya rubuto ne daga Jos ta jihar Filato.
Adireshin imel: [email protected]
Lambar waya: 07062579831