Abuja-Kaduna: Shin farin jinin jirgin ƙasa ya ragu?

Daga NASIRU ADAMU EL-HIKAYA

Kamar yadda hukumar sufurin jirgin ƙasa ta Nijeriya NRC a taƙaice ta ba da sanarwa a ranar Litinin ɗin da ta gabata za ta dawo da sufurin jirgin ƙasa tsakanin Abuja da Kaduna, hakan ya tabbata.

Wannan kuwa tun dakatar da sufurin biyo bayan harin da ’yan ta’adda su ka kai wa ɗaya daga jiragen da ya tashi daga Abuja zuwa Kaduna a ranar 28 ga watan Maris na bana. Kafin dawo da sufurin a Litinin ɗin an so yin hakan a baya amma aka ɗage. Abun dubawa a nan shi ne yadda mutane su ka karɓi dawo da sufurin bayan wancan akasin da ya yi sanadiyyar mutuwar wasu fasinjoji da ma sace wasu har su ka yi watanni kafin samun kuɓuta.

Rahotanni sun nuna ba a samu tururwa a ranar da a ka dawo da sufurin ba. In an kwatanta yadda mutane gabanin harin kan cunkushe tashar Idu da Kubwa a Abuja hakanan da Rigasa a Kaduna don shiga jirgin, za a iya cewa kamar ba mutane ne masu marmarin shiga jirgin.

Wannan ni a waje na ba abun mamaki ba ne don dama mutane na sha’awa da rububin shiga jirgin ne don zuciyarsu ta kwanta da lamarin cewa akwai ingantaccen tsaro da hakan zai sa hankali a kwance mutum zai tafi Kaduna ko ya taho daga Kaduna zuwa Abuja ba tare da ya faɗa tarkon varayin mutane ko wasu ’yan fashi da sauran masu ta’addanci na zamanin yau ba.

Akasin ya sa mutane sun yi la’asar da gano kusan jigin ƙasan ma bai tsira ba duk da kusan a kowane taragu za a ce akwai jami’an tsaro riƙe da makamai don kula da tsaron lafiyar fasinjoji. A lokacin da a ke salama ba don tafiyar ba ta wuce sa’a biyu tsakanin biranen ba, wani ma sai ya yi barci har da minshari kafin a isa tasha.

Duk wanda ya ke shiga jirgin ƙasan a baya ya san mutane na cikin annashuwa da hango tagwayen titin Abuja zuwa Kano cewa can ne mai matsalar ba wannan jirgi mai aminci ba. Jirgin da har da taragun masu hannu da shuni inda kujerun ma na alfarma ne. Cikin jirgin har da masu sayar da lemon kwalba. Ai iya gatar da za a iya yi wa fasinja kenan kamar kwatankwacin yadda a ke samu a jiragen sama.

Akwai wanda ya taba ba ni labarin sun makara shi da wasu fasinjoji a Rigasa da yamma za su taho Abuja sai su ka tarar har jirgin zai fara tafiya. A haka ya ce su ka yi ƙundunbala su ka faxa jirgin don gudun bin hanyar mota da ke da hatsari? Kun ga a irin hakan har raunuka fasinjoji za sui ya samu.

Hatta sayar da tikitin ya kan zama sai mutum ya yi oda da wuri ko kuma ka ga an zo an yi cirko-cirko a na bin dogon layi don samun tikitin. Manyan masu hannu da shuni ciki har da ’yan majalisar dattawa da wakilai na marmarin bin jirgin.

Manyan jami’an tsaro ma ba a bar su a baya ba wajen shiga jirgin na ƙasa da a al’adar Nijeriya tamkar jirgin ƙasa na talakawa ne inda masu sukuni kan shiga jirgin sama ko su ɗauki kwambar manyan motoci da jibgin jami’an su bi hanya ba tsayawa a madakatar mota bare danjar kan titi.

Abun da na tabbatar ya faru ko da a lokacin da a ka kawo sabon sufurin jirgin ƙasan bai hana ɗimbin mutane shiga mota su bi hanyar Abuja zuwa Kaduna ba. Duk ranar da mutum ya gwada bin hanyar zai gamu da abokan tafiya masu yawa. Duk wanda ka tambaya yaya ta hanyar ka bi ka taho sai ya ce ta nan ya bi ai lamarin sai addu’a don yanzu ba sauran babban abu da ya zama garkuwa ga mutane da ya wuce a yi addu’a a kama hanya.

Haryan nan ce fa ke ɗauke da jihohin da ke yanki mai yawan jama’a na arewa maso yamma. Ban da zuwa Kaduna, masu tafiya Kano, Katsina, Zamfara da Sokoto ta nan su ke bi. Hatta masu zuwa Kebbi kan bi hanyar in ka deɓe masu bin sabuwar hanyar nan daga Kontagora zuwa Birnin Kebbi. Muhimmancin sufuri ga rayuwar jama’a ba zai misaltu ba.

Don haka duk rintsi za ka ga mutane na tafiya. Ka gwada ko yau ka shirya tafiya wani gari sai ka samu abokin tafiya wanda shi ma ya shirya a ranar zai yi tafiya. Ko a tarihi lokacin da ba hanyar mota ’yan kasuwa ko fatake na yin doguwar tafiya cikin tawaga riqe da ’yan makamai da za su taimaka wajen tinkarar miyagun iri.

Tawagar kan kama hanya ta yi tafiya ƙarƙashin madugu da kan jagoranci ayarin ’yan kasuwar. Haka da ikon Allah wasu da dama daga ’yan kasuwar kan samu nasarar isa garin da su ka yi nufi lafiya su ci kasuwa su kammala su yiwo sarin kaya su taho gida.

Irin wannan tafiya kan ɗauki kwanaki, makwanni har ma watanni don cin zango da a ke yi da ya ke kuma da kafa a ke tafiya ko kan dabbobi da su ka haɗa da dawaki da jakuna. Wasu daga irin ’yan kasuwar kan zauna ma a wasu garuruwa a kan hanya su kafa sabon muhalli su zauna shikenan sun zama ’yan garin har ma su bar zuriya mai yawa.

Wasu garuruwan ma ta haka su ka ginu daga fatake masu cin zango. Don haka sufuri ba zai yiwu ya tsaya cak ba ko da kuwa akwai wata barazana a hanya. Tsadar man fetur ko ƙarancin motoci masu inganci ba ya dakatar da tafiya. Wani ma ya kan shiga mota da za a sauke shi a hanya ya sake shiga wata har ya isa inda ya yi nufi.

A yanzu ba ramukan kan hanya su ka bi damun fasinjoji ba, a’a zullumin cin karo da ɓarayin mutane. Aa zamanin yau ɓarayin sun fi dogon buri fiye da na baya ’yan kwanta-kwanta da burin su su karve kuɗin matafiya su shige daji. To amma yanzu ba ta guzurin da ke aljifan mutane ke gaban ɓarayin ba, a’a burin su, su shige daji da mutanen a shiga cinikin nawa za a biya su kuɗin fansa kafin sako mutanen.

Duk wannan a Nijeriya ya ke faruwa cikin dazukan da son samu burtalin shanu ne ko gonaki ne ko mazaunan namun daji ne. Miyagun iri sun fi shaggar daji sanin daji a yanzu don labarun yadda barayin kan shiga daji da mutane su share watanni ba tare da an gano su ba abun tsoro ne ainun.

Ba za mu ce kai tsaye gazawar jami’an tsaro ba ne don wai abun da ka ga ya sa shagga faɗawa ruwan zafi to ya fi ruwan zafi. Duk nazari na nuna a na samun baragurbi a kowane ɓangare shi ke sanya rashin samun nasarar amintar da hanyoyin mu daga mugayen mutane.

Kazalika jiragen yaƙi ba zai yiwu su yi ta ruwan wuta a ko ina a dazukan ba don hakan kan jawo garin gyaran gira a tsokale ido ko ma’ana a garin kai hari kan varayin a iya rutsawa da waɗanda a ka kama. Wannan yaƙi ne mai wuyan gaske kuma ya zama wata babbar jarrabawa ta a hankali-hankali ta shigo yankin arewacin Nijeriya.

A shekarun baya ai matafiyi ba ya tsoron yin tafiya dare da rana kuma manomi kan shiga daji ya yi ta nomansa ya na kula da ƙarƙashin lamfo ko akwai maciji ko kunama da za a iya cutar da lafiyarsa, to amma yanzu ga wasu mutane da su ka fi macizai mugunta don kuwa ai an ce in maciji ya sari mutum to mutum ya nemi shiga rayuwarsa ne ko macijin ya firegita ne ya na ƙoƙarin kare kansa.

A ɓangaren mutane masu mugunta ba laifin komai kawai don neman abun duniya za su tare hanya da manyan bindigogi su kama mutanen da ba su san uzurin da ke gabansu ba, su shiga daji da sun a tsawon kwanaki cikin mawuyacin yanayi. A irin haka in akwai mai shan magani ko mai karvar wata allura don wani ciwo da ya ke damunsa sai cutar ta ta’azzara.

Ko titi ka hau in dai ka na da adalci a zuciyarka to ka da ka yi son kai wajen babakere ko ganganci ko tunain kai ka fi kowa uzuri, don ba shakka in dai za a bincika ba mamaki a samu wanda uzurin sa ya fi na ka.

Kammalawa;

Hukumar jiragen ƙasa ta sanya sabbin dokoki na lalle sai mai katin shaidar zama ɗan ƙasa ne zai shiga jirgin bayan sanin lambar wayarsa da sauransu. Wannan na nuna a kan rufe gida da varawo kenan a baya. Ma’ana ta kan yiwu kenan a cikin fasinjoji a kan iya samun waɗanda a ke zargi da zama miyagun iri ko ma ’yan ta’adda ko masu ba su labari. Fatar a nan hakan ya yi tasiri wajen kare lafiyar jama’a.

Kuma gwamnati ta ƙara dagewa wajen aminta dajin da ma hanyar Abuja zuwa Kaduna don amfanin masu shiga mota. Rahotanni na nuna ɓarayin sun ɓulla a gefen hanyoyin Kaduna ta kudu kan hanyar Abuja-Keffi-Gidan Waya zuwa Hawan Kibo. Kullum fasinja ya rungumi addu’a makamin bawa.