AFCON 2024: Tawaga takwas sun sami gurbin shiga gasar

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Tawagar Ƙwallon Ƙafa takwas sun sami gurbin buga gasar kofin nahiyar Afirka da Ivory Coast za ta karvi baƙunci a 2024.

Masar ce ta takwas da ta samu gurbin tawaga 24 da za su kece raini a baɗi, bayan da ta ci Guinea 2-1 ranar Laraba.

Kenan Masar za ta kafa tarihin shiga gasar karo na 26, ba wadda ta kai ƙasar yawan buga wasanni a gasar.

Masar ce ta ja ragamar rukuni na huɗu da maki 12, kuma saura wasa ɗaya ya rage a kammala karawar cikin rukuni, inda Guinea ta ke ta biyu da maki tara.

Waɗanda suka kai bantensu a gasar da za a buga a cikin watan Janairun 2024 sun haɗa da mai riqe da kofin, Senegal da Algeria da Tunisia da Afirka ta Kudu.

Sauran sun haɗa da Morocco da Burkina Faso da kuma Ivory Coast, wadda ita ce za ta karvi baƙuncin fafatawar.

Ranar Asabar da kuma Lahadi ake sa ran kammala wasannin cikin rukuni don tantance tawaga 24 da za ta buga gasar kofin Afirka.

Ƙasashe biyu ne daga kowanne rukuni za su samu tikitin shiga wasannin da za a yi a 2024 a Ivory Coast.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *