Ahmed Musa ya jefa Ronaldo da Al-Nassr cikin matsala

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta Duniya (FIFA) ta haramta wa Al-Nassr rajistar sabbin ’yan wasa saboda rashin biyan wasu kuɗaɗen da Leicester City ke bin ta a wani ɓangare na yarjejeniyar Ahmed Musa.

Al-Nassr ya sayi Cristiano Ronaldo ne a watan Janairun 2023 amma FIFA ta dakatar da ita daga sake yin rajistar sabbin ’yan wasa sakamakon taqaddama ƙungiyar Leicester.

Hakan ya faru ne sakamakon gazawar kulob ɗin Saudiyyar na kasa biyan ƙungiyar Leicester ƙarin kuɗaɗe dangane da yarjejeniyar da ta yi da ɗan wasan Nijeriya, Ahmad Musa.

Tsohon ɗan wasan gaban CSKA Moscow ya koma Foxes nan da nan bayan da ƙungiyar ta lashe gasar firiya a kakar wasa ta 2015/16 amma bai samu nasara ba ko kaɗan a Ingila.

Kyaftin ɗin na Super Eagles ya zura ƙwallaye biyar a wasanni 33 da ya buga a dukkanin gasa da Foxes kafin a bar shi ya koma tsohuwar ƙungiyarsa a matsayin aro.

Daga nan ne aka sayar da Musa ga Al-Nassr kan kuɗi fam miliyan 14 a kasuwar musayar ‘yan wasa ta shekarar 2018.

Musa ya buga wa Al-Nassr wasanni 60 kuma ya lashe gasar kafin a sake shi a matsayin wakili na kyauta bayan shekaru biyu.

Hukunci a hukumance daga FIFA ya yi ikirarin cewa ƙungiyar ta Saudiyya ta gaza biyan Yuro 460k (£ 390k) tare da sha’awar aarin abubuwan da suka shafi wasanni.

Tun da farko dai an fitar da hukuncin ne a watan Oktoban 2021, inda aka gargaɗi Al-Nassr cewa za a sanya mata takunkumin yin rajistar canja wuri idan har ta kasa biyan Leicester wasu maƙudan kuɗaɗe.

Yanzu dai ana kyautata zaton kulob ta ya gaza wajen bin wannan hukunci kuma an sanya masa dokar hana yin rajista.

Wannan ya shafi canja wuri na gida da na waje, ma’ana tauraro daga ƙetare ba za a iya yin rijistar a ƙungiyar ba a halin yanzu ba.