Akwai rufin asiri a cikin sana’ar fawa – Sarkin Fawa Usaini

Daga DAUDA USMAN a Legas

Sarkin fawar ƙaramar hukumar Amuwo Odofin a Legas, Alhaji Usaini Iliyasu bakin sabuwar kasuwar Bichi mazaunin Legas wanda yake gudanar da harkokin kasuwancin sana’ar fawa akan titin Bila fak tasakwan rebo kusa da Mile 12 titin a cikin birnin Legas, ya bayyana cewar akwai rufin asirin Ubangiji a cikin sana’ar fawa idan aka tsare gaskiya da riƙon amana.

Sarkin fawan, Alhaji Usaini Iliyasu bakin sabuwar kasuwar Bichi wanda ya bayyana hakan a ofishin sa dake Bila fak jim kaɗan bayan kammala taron su da waɗansu mahautan kasuwannin cikin garin Legas waɗanda suka zo masa murnar gudanar da taron walimar auren sa da amaryar sa Fatima Usaini wanda aka ɗaura a unguwar Jabiri ta ƙaramar hukumar Funtuwa a jihar Katsina a ƙarshen makon jiya.

Ya bayyana wa jaridar Manhaja a Legas farin cikin sa da jin daɗin sa a gam da wannan al’amari, ya cigaba da cewa babu shakka yana isar da saƙon godiyar sa ga dukkan mahauta da sauran al’ummar dake cikin garin Legas waɗanda suka zo taya shi murnar gudanar da wannan taro, da fatan kowa ya koma gidan sa lafiya.

Usaini ya cigaba da shawartar mahautan jihar Legas da Nijeriya baki ɗaya da su cigaba da sanya ’ya’yansu makarantun boko da Arabiya domin ‘ya’yan nasu su samu ilimin ɓangarorin guda biyu.

Haka zalika ya qara da cewar mahautan su cigaba da riƙon amana tare da tsoron Allah a lokacin da suke gudanar da harkokin sana’ar su ta fawa a kowanne lokaci domin samun kyakkyawar riba anan duniya dama lahira baki ɗaya.

Ya ci gaba da kira ga mahauta mazauna jihar Legas da sauran jihohin kudu da yammacin Nijeriya da su cigaba da zaman lafiya da sauran ƙabilun da suke zaune da su a yankunan jihohin da suke zaune da su gaba ɗaya.

A ƙarshe, Sarkin fawan na sakwan rebo abila fak ya ce ya kamata ‘yan Nijeriya su ƙara ƙoƙari wajen gudanar da addu’o’in neman karin zaunar da ƙasar nan lafiya.