Kotu ta bada umarnin dawo da shaidar farko a shari’ar Sheikh Abdujjabar

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano

A safiyar ranar Alhamis ne aka ci gaba da gabatar da shari’ar Malamin Addinin Musulunci, Sheikh Abdujabbar Nasir Kabara, wanda aka gurfanar da shi a gaban kotun shari’ar Musulumci da ke zaman ta a Ƙofar Kudu a jihar Kano.

A zaman kutun, Barista A. O. Mohammed (SAN) ne ya jagorance lauyoyin da suke kare Malam Abdujabbar, inda Barista Sa’ida Shu’aibu (SAN) ya jagoranci tawagar lauyoyin masu gabatar da ƙara.

Lauyoyin malamin sun nemi a dawo musu da shaidar farko, domin sake yi masa tambayoyi, sai dai vangaren da suke gabatar da ƙara sun yi suka akan wannan roƙo, inda suka nuna cewa, hakan ya saɓa da ƙa’ida kuma vata lokacin kotu ne.

“Wannan shaida na ɗaya an sallame shi. A yanzu haka yana makarantarsu a Jamhuriyyar Nijar. A tsari na shari’a Allah maɗaukakin sarki ya hana wahalar da shaida,” inji Sa’ida Shu’aibu.

Ya ƙara da cewa, “idan muka duba dokar ACJL 2019 sashe na 258, ya nuna cewar wajibi a kawo ƙwararan dalilai da za su sa a yi wa shaida kiranye, in akwai ɓata lokaci koda an kawo ƙwarraran dalilai, to kotu ba za ta yarda ba. Sati 4 da aka bayar ya nuna ɓata lokaci ne hakan daga gare su.”

A nashi martanin, Barista A. O. Mohammed SAN ya ce, roƙon da ya yi ƙanƙanin abu ne suka maida shi babba kuma ba haka dokar ta ce ba.

“Domin a sashe na 258 ACJL ya bada dama a dawo da shaidar a kowanne lokaci, idan kotu ta ga dama da kanta ko kuma duk lokacin da wani daga ’yan shari’a ya yi nema na a dawo da shi,” inji A.O Mohammed SAN.

Mai Shari’a Ibrahim Sarki Yola bayan ya nazarci hujjojin dukkan ɓangarorin, ya bayyana cewa, wannan roƙo bai saɓa da doka ba.

“Wannan roƙo bai saɓa da doka ba. Shi ya fi kama da adalci. Sashe na 258 ACJL ya ƙarfafe su ne da cewa a kowane lokaci, alƙali ko ɗan shari’a ya yi roƙo a dawo da shaida, za a iya dawo da shi. Na bi ƙa’ida kuma na kwatanta adalci,” inji Mai Shari’a.

Sannan ya bada umarnin a dawo da shaidar a zama na gaba, don sake yi masa tambayoyi a shari’ar.

Daga ƙarshe dai mai shari’a Sarki Yola ya ɗage shari’ar zuwa 17 ga Fabrairu, 2022, don cigaba da shari’ar.