Amfanin zogale ga lafiyar iyali

Daga BILKISU YUSUF ALI

Tambaya:
Salam. Anti Bilkisu, Ina da tambaya kan muhimmancin zogale ga lafiya, musamman lafiyar iyali.

Amsa:
Zogale yana da matuƙar amfani a jikin ɗan’adam don haka masana kiwon lafiya suke yawan ambatonsa a wurin magance ƙanana da manyan cutoci. Zogale yana da tasiri Allah Subhanahu wata’ala Ya yi masa albarka kasancewar bincike-binciken kimiyya sun tabbatar da cewa yana da amfani a fannoni da dama. A kimiyance ana yi wa zogale laƙabi da Moringa oleifera wato Drumstick tree a Turance.

Zogale yana da tasiri kwarai a jiki amma fa yana da ƙa’ida wajen shanya shi ba a son a shanya shi a rana saboda rana tana kashe sinadaransa masu amfani a jiki, sannan kuma saboda ingancin tsafta ana so a shanya shi ne a inuwa ko ma ɗaki cikin ingantacciyar tsafta.

Daga cikin magungunan da zogale yake yi akwai:-

•Cin zogale wanda aka turara yana ƙara wa mai shayarwa ruwan nono.

*Ga mai ciwon Suga ana samun garinsa cokali guda babba a sa a abinci a ci a mai-maita a rana sau biyu. In sha Allah za a samu lafiya in har an dimanci hakan.

•Ga namijin da yake da rauni ana samun zogale busasshe da citta da kanumfari da da garin ɗanbashanana da citta mai ‘ya’ya da tafarnuwa a dake su ana iya ƙara sinadarin ɗanɗano da gishiri a ake sa wa a miya ko a madara mai ɗimi ake sha kullum sau ɗaya.

•Ga mai fama da lararurar ulcer ana amfani da zogale garinsa a haɗa zuma ko madara ake sha kafin a ci abinci.

•Ga mai tsutsar ciki ana samun ɗanyen zogale a matse shi a sha yana magance larurar tsutsar ciki.

•Ga waɗanda ke fama da ƙarancin jini ake son jininsu ya ƙaru su lizimci cin zogale da shan ruwan da aka dafa zogalen in sha Allah za a dace.

Za mu ci gaba mako mai zuwa insha Allah.

Ga mai neman ƙarin bayani ko tambaya kan wani abu da ya shafi lafiyar iyali yana iya aiko da tambayarsa ta hanyar wannan lambar 08039475191 ko ta shafina na ‘Facebook’ mai suna Bilkisu Yusuf Ali ko a ‘Facebook Account’ ɗina, Bilkisu Yusuf Ali.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *