AMPAT ta nemi majalisar Kano ta zartar da doka mai tsanani kan masu kwacen waya

Daga IBRAHIM MUHAMMAD a Kano

Ƙungiyar Masu Hada-hadar Wayoyin Hannu ta Jihar Kano (AMPAT), ta yi kira ga majalisar jihar da su samar da doka mai tsanani da za ta riƙa hukunta masu kwacen waya a Kano.

Kakakin ƙungiyar, Alhaji Ashiru Yusuf Yakasai ne ya yi wannan kiran.

Ya yi nuni da cewa rashin tsatsauran matakin hukunci na doka na taimakawa wajen ta’azzarar kwacen wayoyin da ɓata gari suke.

Ya ce, masu kwacen wayar sukan yi sanadin lahanta mutane da jawo asarar rayuka wanda mummunar ta’adar tasu ba shi da maraba da fashi da makami.

Alhaji Ashiru Yusuf Yakasai ya ce, a yanzu jami’an tsaro suna iya ƙoƙarinsu wajen kama masu kwacen, amma idan aka yanke musu hukunci sai su dawo su cigaba. Samarwa da kuma zartar da tsatsauran doka ne zai taimakawa wajen kawo ƙarshen masu kwacen.