Dandalin shawara: Ƙawa nake so kyakyawa kuma mai kuɗi

Daga AISHA ASAS

Salam. Asas ina wuni. Ya aiki. Ki daure ki amsa tambaya ta don Allah. Tun kwanaki na yi ta turowa kina share ni. Don darajar iyayenki ki duba lamari na. Na kasance tun Ina ƙarama ban yi sa’ar ƙawaye ba, don ba su sona saboda Allah. Da na girma suka yi ta min ababe da dama na cutarwa. Har na haqura a farko, sai dai na ce bari na neme ki shawara, don Allah yadda zan samu ƙawa ta gari, mai kyau kuma wadda gidansu masu kuɗi ne, don kada ta so ni don abinda na ke da shi. Don Allah Ina jiran amsa. Na gode. (Wannan rubutun kaso mafi rinjaye ya zo ne cikin harshen Turanci, don haka kamar yadda lokuta da dama sai mun gyara rubutun da aka turo kafin mu dora, wannan ma haka).

AMSA:

Da farko dai zan so in fara da tambaya zuwa gare ki, don ƙara tabbatarwa ba fahimtar tambayar ta ki na yi ba daidai ba. Shin ƙawa da za ku dinga alaƙa ta zumunta tsakanin ku, tare da sanar da juna damuwar ku, da kuma raba farin cikin ku a tsakanin juna, sannan ya zama alƙawari tsakanin ku cewa, ɗaya ba zai ci amanar ɗaya ba, ba zai cutar da ɗaya ba, zai kare mutunci da darajar ɗaya ko da ba idon ɗayan. Shin wannan irin ƙawar ki ke nufi ko kuwa mijin aure ki ke magana kai.

Dalilin tambayar kuwa sharuɗan da ki ka zayyano sun fi kama da siffar da za a iya buqata a tattare da mijin aure ko matar da ka ke burin aura.

Tun daga farko, zan iya cewa, kin yi wa kalmar ƙawance gurguwar fahimta, saboda a cikin muradun ki, guda ɗaya ne kawai ake buƙata ga ƙawar da za a so ƙawance da ita, wato ƙawa ta gari. Sannan a farkon farawa, kin bayyana rashin sa’ar ƙawaye da kalmar ‘rashin samun ƙawa da ke sonki don Allah’. Shin son wadda ke da kyau ko dukiya shi menene?

Son mutum don Allah na nufin amsar sa ba tare da sharaɗi ba, na daga duba da halitta ko nauyin aljihunsa ba. So don Allah na nufin, duba da halayyar abokin zama, ma’ana son shi don yana mutumin kirki, mai ƙoƙarin kusanta kansa da hanya madaidaiciya.

Ƙawa ta gari ita ce, mai son ƙawarta saboda tana ita, ba don tana wata ba. Mai riƙe sirrin ta, mai tausaya mata a lokacin damuwa, mai farin ciki yayin da ta samu cigaba a rayuwa, mai sanar da ita gaskiya koda bata son jin ta, mai rikiɗewa ta zama ita a lokacin da ba ta kusa, ta hanyar kare mutuncin ta, tare da tabbatarwa babu mai faɗar aibun ta ba tare da ta yi ƙoƙarin wanke ta ba.

Ƙawa ta gari ita ce, mai kallonka ba komai ba, a lokacin da ka ke komai, ta hanyar duban tsabar idonki ta sanar da ke ba ki kyauta ba idan kin yi ba daidai ba, a daidai lokacin da mutane da yawa ke shayin sanar da ke hakan.

Ƙawa ta gari ita ce, mai wurgi da kyawon da ki ke da shi, ta hanyar ɗaukar shi ba a bakin komai ba a cikin zamantakewar ku, wanda hakan zai sa ko da shi, ko babu shi za ta iya zama da ke.

Ƙawa ta gari ita ce, mai ƙin bambance samu da rashi, ciwo da lafiya, ƙunci da farin ciki, domin a kowanne yanayi ba za ta bar ki ba. Kuma tana iya sadaukar da nata farin ciki don samar da na ki.

Idan har kin fita a wannan dogon layin, to ba ki kasance daga cikin ƙawaye na gari ba, kuma idan har ba waɗannan ne alƙiblarki a zaɓin ƙawa ba, to fa wani abu daban ki ke nema, amma ba ƙawa ta gari ba.

Shawara, idan kina neman irin wannan ƙawa, to ki fara da zama irin ta kafin ki neme ta, ma’ana ki canja ra’ayin ki kafin ki cancanci wannan matsayi.

Sau da yawa muna karaɗe kunnuwan mutane da cin amanar ƙawayenmu gare mu, ko rashin riƙe mana amana da suke yi, amma ba ma faɗar namu halin da yadda muka zauna da su, ko tambayar kanmu shin ba za mu iya yi masu abinda suka yi mana idan mun samu dama.

Allah Ya sa mu dace.