Matsalolin haƙora da yadda za a magance su (2)

Daga AISHA ASAS

A satin da ya gabata mun kawo wasu daga cikin matsalolin haƙora da kuma yadda za a iya magance su ta hanyar amfani da tumfafiya.

Idan mai karatu bai manta ba, mun fara da matsalar haƙora mai ciwo da yadda za a iya magance shi, sai kuma matsalar kogon haƙora da yadda ake amfani da tumfafiya wurin samun sauƙi ga mai fama da lalurar.

A wannan satin, da yardar mai kowa, za mu kawo ƙarin wasu daga cikin matsalolin da kuma yadda za a iya samar da waraka ta hanyar amfani da tumfafiya.

Idan mun koma kan matsalar tsutsar haƙori, ita ma za a iya amfani da tumfafiya don samun sauqi daga matsalar. Ta yaya? Za a tafasa saiwar tumfafiya a kuskure baki da ruwan suna masu ɗumi, safe da dare, tsayin kwanaki uku.

A wasu lokuta kana iya samun kanka a jerin masu matsalar fitar jini daga haƙoranka, ya Allah ta sanadiyyar motsa haƙoran da yawa, kamar ƙaramin duka a baki, ko ƙoƙarin cire wani abu da ya maqale a tsakanin haƙora, kamar nama.

Duk da cewa, sau da yawa kogon haƙora na tsakanin haƙori da haƙori kan iya haifar da zubar jini, a sa’ilin da wani abinci ya samu gurbin zama a wurin, lokuta da dama idan ka yi yunƙurin cire shi ko bayan ka cire shi, jini kan biyo baya, wani sa’in har da ciwo. Baya ga wannan matsala, akwai ta rashin tsaftace baki yadda ya kamata, wannan kuwa magance ta na tasiri ne bayan an yawaita tsaftace haƙoran.

Sai kuma akwai cutar haƙori mai zaman kanta ta zubar da jini lokaci-lokaci, wani sa’in ma ba wani dalili daga cikin dalilan da aka jero a sama. A wannan gava muna magana ne kan ita wannan cuta mai haifar da zubar jini a baki. Idan kuna tare da ita, sai ku samu ganyen tumfafiya tare da sassaƙen ta, kanunfari kaɗan da kuma ɗan gishiri.

Za a dafa cikin ruwa mai tsafta, sai a dinga kuskura baki da ruwan a lokacin da zafin su ya yi daidai da yadda baki zai iya amsa. Ana aikata hakan safe da kuma dare Idan za a kwanta.