Ganduje ya yi abin a yaba, cewar Sarkin Kano

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano

Sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero, ya ce Gwamna Abdullahi Umar Ganduje mai barin gado ya yi abin a yaba a tsawon shekara takwas da ya yi yana mulkin jihar.

Badaraken ya ce Jihar Kano ta samu gagarumin cigaba a zamanin mulkin Ganduje, kuma Masarautar Kano ta ba wa gwamnan cikakken goyon baya wajen cimma hakan.

A cewarsa, Ganduje ya ƙirƙiro tare da aiwatar da muhimman ayyukan cigaba da dama waɗanda suka shafi rayuwar Kanawa ta fuskoki daban-daban.

Ya bayyana haka ne a jawabinsa na Hawan Nasarawa, inda ya ziyarci gidan gwamnaitn jihar a ranar Lahadi.

Sakataren yaɗa labaran Mataimakin Gwamna, Hassan Musa, ya ruwaito cewa Sarkin Kano ya bayyana godiya ga Gwamnan bisa yadda ya ba shi damar zama magajin kakanninsa, a kan sarautar Kano.

“Ba za mu taɓa manta irin alherin da ka yi mana ba. Muna roƙon Allah Ya ci gaba da ɗaukaka ka, ya yi maka jagora a cikin duk al’amuranka,” in ji Sarkin.

Rahotanni sun ce sarkin ya yi kira ga al’ummar masarautar da su bayar da haɗin kai ga aikin ƙidayar jama’a da za a gudanar a watan Mayu.

A nasa ɓangaren, Gwamnan Ganduje, wanda Mataimakinsa, Nasiru Yusuf Gawuna, ya wakilta, ya yaba da irin goyon bayan da Masarautar Kano ta ba shi domin gudanar da ayyuka da shirye-shiryen gwamnati cikin nasara.

Ga ƙarin hotuna daga hawan da sarkin ya yi: