An kashe ‘yan bindiga bakwai a Zamfara

Dakarun Rundunar Operation Hadarin Daji a Jihar Zamfara, sun kashe ‘yan bindiga bakwai tare da cake wasu biyu da ake zargin ‘yan ta’adda ne.

Mai magana da yawun rundunar tsaro, Manjo-Janar Musa Danmadami ne ya bayyana hakan cikin sanarwar da ya fitar ranar Lahadi.

A cewar sanarwar, “Dakarun Rundunar Operation Hadarin Daji sun gamu da ‘yan bindiga yayin aikin kakkaɓe ‘yan ta’adda da suka yi ran 22 ga Afrilu, 2023, a yankunan Birnin Tsaba da Tsanu da Lamba da Gabas da Gidan Kaso da kuma Dajin Dumburum cikin Ƙaramar Hukumar Zurmi, Jihar Zamfara.”

Sanarwar ta ƙara da cewa, an lalata maɓuyar ‘yan bindigar da dama a yankin.

Haka nan, ta ce abubuwan da aka ƙwace daga hannunsu har da babura guda bakwai da bindiga ƙirar AK 47 guda biyu da sauransu.

“Biyo bayan damƙe wani mai taimaka musu da bayanai da aka yi a ranar 21 ga Afrilun 2023, sojoji sun gudanar da aiki inda suka cafke mutum biyu a garin Shinkafi cikin Ƙaramar Hukumar Shinkafi, Jihar Zamfara,” in ji sanarwar.

Kayayyakin da aka ƙwace daga hannunsu sun haɗa da babur ɗaya da wayar salula guda uku.

Rundunar sojijin dai ta sha faɗa a lokuta da dama cewa ba za ta yi ƙasa a gwiwa ba wajen ganin bayan ‘yan ta’adda a faɗin ƙasar nan.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *