Zargin mu’ammala da ‘yan ta’adda: Gwamnan Zamfara ya maida wa Sarkin Yandoto rawanisa

Gwamnan Jihar Zamfara, Bello Matawalle, ya amince da maida wa Sarkin Birnin Yandoto, Aliyu Marafa, rawaninsa bayan dakatar da shi da aka yi.

Idan ba a manta ba, a baya an dakatar da Marafa ne sakamakon naɗa ɗan ta’dda, Ado Aliero, da ya yi a matsayin Sarkin Fulani a watan Yulin 2022.

Wanda a sakamakon hakan gwamnatin jihar ta kafa kwamitin na musamman domin gudanar da bincike kan abin da Sarkin ya aikata.

Sai dai, sanarwar da Sakataren Gwamnatin Zamfara, Kabir Balarabe, ya fitar, ta ce an maida Marafa kan muƙaminsa bayan sakamakon binciken kwamitin ya nuna Sarkin ba shi da wata mummunar manufa.

A cewar sanarwar, “Mai Girma Gwamnan Jihar Zamfara, Bello Matawalle, ya amince da a maida wa Aliyu Marafa muƙaminsa a matsayin Sarkin Birnin Yandoto.

“Hakan ya biyo bayan shawarwarin da Kwamitin Binciken da aka kafa ya bayar bayan kammala bincikensa game da batun naɗin da Sarkin ya yi wa ɗan ta’adda, Ado Aleiru.

“Kwamitin bai samu wata hujjar cewa Sarkin ya aikata hakan ne da mummunar manufa, ko kuma wani haɗin baki tsakanin Sarkin da ɗan ta’addan.”

Sanarwar ta ƙara da cewa maido da sarkin ya fara aiki ne nan take.