An bai wa tsofaffin sarakunan Kano sa’o’i 48 su fice daga masarautu

Daga IBRAHIM HAMISU, a Kano

Gwamnatin jihar Kano ta bai wa tsofaffin sarakunan masarautun Kano; Rano da Gaya da Bichi da Ƙaraye wa’adin sa’o’i 48 su fice daga fada bayan rushe masarautun da gwamnatin ta yi a ranar Alhamis.

Gwamnan jihar, Abba Kabir Yusuf ne ya sanar da haka lokacin da ya yi jawabi jim kaɗan bayan sanya hannu kan dokar da ta rushe dokar da ta assasa masarautun a shekara ta 2019.

A ranar Alhamis ne Gwamnan ya sanya hannu kan sabuwar dokar masarautar Kano, wadda ta rushe ƙarin masarautu huɗu da aka samar a 2019, wanda hakan ya sanya suka rasa muƙamansu na sarakunan jihar masu daraja ta ɗaya.

Gwamna Abba Kabir ya ce, “Ina umartar sarakunan da dokar ta shafa su fice daga fadojin cikin sa’o’i 48”.

Sarakunan da aka sauke su ne: Sarkin Kano Aminu Ado Bayero, Sarkin Bichi Nasiru Ado Bayero, Sarkin Rano Kabiru Muhammad Inuwa, Sarkin Gaya Aliyu Ibrahim Abdulkadir, sai kuma Sarkin Karaye Dr Ibrahim Abubakar.

Masanin tarihin Kano, Mal. Ibrahim Ado Kurawa, ya ce, soke dokar masarautu da Ganduje ya yi ita ce daidai.

Kurawa ya ce, “Sarautar Kano abu ne wanda aka gaje shi kafin Bature ya zo kuma da Bature ya zo ya bar shi don haka ba za a ƙirƙiro abin da babu shi ba, shi ya sa tsohon Gwamnan Kano Ganduje ya zo ya yi wannan wanda akwai shirme da yawa a ciki abubuwan da aka sansu ya lalata su, saboda haka wannan dama ce aka samu don a maida abubuwa yadda suke na asali.

“Waɗannan abubuwa da Ganduje ya ƙirƙiro babu su kafin jihadin Shehu Usman Danfodiyo kumaya yi wadannan ne don ya ɓata abinda ya tarar tunda a tunaninsa shima zai yi abin da Ɗanfoyo ya yi , to Alhamdullahi yanzu Allah Ya kawo lokacin da majalisa za ta gyara a koma yadda ake na asali”. Inji Ibrahim Ado Kurawa.

Da ya ke tofa albarkacin bakinsa, Nazifi Nura mazaunin cikin garin Kano ya ce, bai ji daɗi ba a kan cire sarakunan da aka yi inda ya ce, “Mu wannan abu ba mu ji daɗinsa ba domin duk mai ƙaunar Kano ba zai yi farinciki da wannan cire sarakunan ba.

“Domin idan aka ta sanadiyyarsu an samu cigaba sosai, misali kamar Bichi yanzu ɗan Katsina anan ya ke tsayawa ya sayi fili saboda idan cigaban da ta samu, Bichi yanzu kamar Kano ta ke, haka idan ka je Rano haka Gaya, fiye da shekara 30 Gaya ba ta samun cigaba, amma saboda sabanin sarakunan Gaya ta samu matuka ga ita Kanta Karaye, don haka maganar gaskiya ba ma murna da wannan rushe masarautun”.