An cafke mutum 5 bisa zargin cin naman mutune a Zamfara

Daga WKAILINMU

A ranar Talatar da ta gabata ne a Jihar Zamfara aka gurfanar da wasu mutum biyar a gaban kotun majistare mai lamba ɗaya a Gusau, bisa zarginsu da kashewa tare da cin naman wani yaro.

Daga cikin waɗanda aka gurfanar ɗin kuma ake zargi, har da wani fitaccen dillalin motoci a Jihar.

Ana dai zarginsu ne da kashewa sannan suka ci naman Ahmad Yakubu Aliyu, wani yaro mai kimanin shekara tara a duniya.

An dai kawo mutanen da ake zargi ne gaban kotun cikin tsauraran matakan tsaro.

Sai dai bayan da alƙalin kotun, Mai Shari’a Sa’adu Gurbin Bore ya karanta musu laifukan da ake tuhumarsu da su, sun musanta aikata ko ɗaya daga ciki.

Daga nan ne ya ɗage ci gaba da sauraron ƙarar har zuwa ranar takwas ga watan Fabrairun 2022 mai zuwa.

Iyayen yaron da sauran masu jajanta musu dai sun yi cincirindo a harabar kotun suna neman a hukunta waɗanda ake zargin, inda suka ce lamarin abin takaici ne matuƙa.

Mahaifiyar yaron, wacce ta bayyana sunanta a matsayin Jamila Abdurrahman, ta shaida wa menama labarai cewa, sun je kotun ne don bin kadin jinin ɗansu, da kuma tabbatar da cewa bai tafi a banza ba.

Daga nan ne sai alƙalin kotun ya aika da mutum uku daga cikin waɗanda ake zargin zuwa gidan yari, yayin da ragowar biyun kuma ya aika da su gidan horar da kangararrun yara saboda ƙarancin shekarunsu.