Zan miƙa lafiyayyiyar ƙasa ga magajina – Buhari

*Za mu taya ka da addu’a, cewar Sarkin Musulmi

Daga AMINU AMANAWA a Sakkwato

Shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari ya ci alwashin cewa, zai miƙa lafiyayyiyar ƙasa mai cike da zaman lafiya da kwanciyar hankali tare da yalwar arziki ga magajinsa a shekara ta 2023, inda Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Sa’ad Abubakar III, ya ci alwashin taimaka wa Shugaban Ƙasar da addu’o’i tare da kuma dukkan goyon bayan da suka kamata.

Kalaman na Shugaba Buhari su na zuwa ne a yayin ziyarar aiki ta kwana ɗaya da ya kai a Sakkwato jiya; ziyarar da ke da manufar ƙaddamar da kamfanin siminti mai samar da tan miliyan uku da kamfanin siminta na BUA ya samar a Sakkwato, duk da matsalar tsaro da wasu ƙananan hukumomin jihar ke fuskanta, musamman ma na gabashin Sakkwato da wasu sassan su ke maƙwabtaka da Jihar Zamfara da ma wani sashe na Jamhuriyar Nijar.

Koda yake bayanai daga fadar ta Shugabann Ƙasa tunda farko sun nunar da cewa, Shugaba Buhari zai ziyarci Jihar Sakkwato, domin ƙaddamar da kamfaninin siminti na BUA, inda daga bisani kuma ya wuce Zamfara, domin duba halin da yanayin tsaron jihar ke ciki; ziyarar da shugaban ya dakatar saboda sauyin yanayi maras kyau.

Isar tawagar shugaban filin tashi da saukar jiragen sama na Sarkin Musulmi Abubakar III ke da wuya, shugaban ya zarce zuwa fadar Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar III, tare da rakiyar Gwamnan Jihar Sakkawato, Rt. Hon. Aminu Waziri Tambuwal, da gwamnonin jihohin Kano da Kebbi da kuma sauran muƙarabban gwamnati.

A yayin da ya ke jawabi a lokacin da ya ziyarci fadar ta Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya bayyana damuwarsa kan matsalar tsaro sakamakon irin abubuwan da suke faruwa na matsalar tsaro a Arewa maso Yamma.

“Ko wace rana ta Allah mu na cikin damuwa kan abinda ke faruwa a jihohin Arewa maso Yamma, kuma koda mu ka ɗare madafun iko, idan al’ummar Nijeriya za su yi ma na adalci, sun san da irin matsalolin da ke faruwa a Arewa maso Gabas da Kudu maso Kudu, to amma abinda ke faruwa yanzu haka a Arewa maso Yamma abun damuwa ne matuƙa, domin al’ummomin yankin kusan ɗaya ne, al’adunsu ma haka, amma duk da hakan ake samun rashin zaman lafiya da kashe-kashe da satar kayan al’umma. Wa iyazu billah! Allah ya sauwaƙe,” inji Shugaba Buhari.

Bisa wannan ne shugaban ya sha alwashin duk mai yiwa wajen kawo ƙarshen matsalar ta tsaro.

“Za mu yi iyakacin ƙoƙarinmu wajen kawo ƙarshen matsalar, domin tuni mu ka ba wa jami’an tsaro umarni na kada su aga ƙafa ga kan kowane ɗan bindiga, kuma da yardar Allah za mu miƙa ƙasar nan a matsayin mafi zaman lafiya ga waɗanda za su gaje ni.”

Shi ma da ya ke maganuawa, Mai Alfarma Aarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar, ya bayar da tabbacin bada goyon baya, domin samun wannan nasara a haƙilon da ake yi wajen daƙile matsalar tsaro a Nijeriya.

“Ina mai tabbatar maku cewa, za mu ba ku goyon bayan duk da ku ke buƙata da sauran gwamnatoci a dukkanin matakai ta hanyar yin addu’o’i da bada shawarwarin da suka dace.”

Ƙananan hukumomin Isa, Sabon Birni, Goronyo da sauran ƙananan hukumomin da ke gabashin Sakkwaton na daga cikin yankunan da matsalar tsaron ta fi ta’azzara a jihar, inda ko a kwanan baya sai da wasu ’yan bindiga suka qone kurmus motar matafiya a Gabashin Sakkwaton, abinda ya janyo cece-kuce a tsakanin Sakkwatawa na rashin kai ziyarar jaje da kansa daga Shugaban Ƙasa Buhari, duk kuwa da cewa ya aike da ƙaƙƙarfar tawaga a madadin Gwamnatin Tarayyar a lokacin zuwa jihar.