Yan sanda sun kama masu garkuwa 14 a Jihar Jigawa

Daga UMAR AKILU MAJERI a Dutse

’Yan sanda sun kama mutane 14 da ake zargi da garkuwa da mutane tare bindigogi ƙirar AK47 guda uku da kuɗi sama da Naira miliyan biyu. 

Jawabin hakan ya fito ne daga bakin kakakin rundunar ‘yan sanda Lawan Shisu Adam, inda ya ce sun samu narasa wajen kama su bayan sun yi musayar wuta da waɗanda ake zargin.
‘Yan sandan sun fatattake su a yayin musayar wutar har sun harbi ɗaya a ƙafa.

Lawan Shisu ya ci gaba da cewar sun gano maɓoyar ‘yan ta’addar ne a dajin Ɗangwanki da kuma ƙauyen ‘yan damo dukkansu a cikin Ƙaramar Hukumar Sule Tankarkar, inda suke garkuwa da mutane suke amsar kuɗin fansa. 

A yayin misayar wutar, ‘yan sanda sun samu nasarar ƙwato wata mata mai suna Hadiza Alhaji Chadi wadda ta daɗe kwanaki masu yawa tana tare da su, suna neman kuɗin fansa Naira miliyan goma daga mijinta.

Hadiza ta ce a lokacin da suka je gidansu a ƙauyen Marma da ke Ƙaramar Hukumar Kiri Kasamma da misalin ƙarfe biyun dare ba ita suka je sacewa ba, mijinta suka yi niyyar sata amma ba su yi sa’a ba shi ne suka goyata a babur.

Hadiza ta ce sun kai awa uku suna tafiya da ita a daji kafin su isa maɓoyarsu da suke ɓoye mutane, kuma tunda suka kaita ba su taɓa yi mata maganar banza ba, kuma ba su dake ta ba.

Da yake ƙarin haske, Kakakin rundunar ‘yan sandan ya ce ‘yan sandan na jihar ta Jigawa sun yi nasarar kame masu garkuwa da mutanen da iyalansu har su goma sha huɗu, inda suke voye waɗanda suka sato yayin da suka ji wa mutane biyu daga cikinsu rauni a yayin musayar wuta da ‘yan sanda. 

Waɗanda aka kama ɗin sun haɗa da: Sulaiman Abdullahi, Sulaiman Bello, Auwalu Muhammad, Babandi Muhd, Mujitafa Manman, Yakubu Muhd, Musa Mamman, Ardo Manman Audu, Ya’u Haɓe, Bashir Ibrahim, Zilai Hamza, Amina Saminu, Sabira Hamza da kuma Aisha Mohd. 

Kakin dundunar ‘yan sandan ya ƙara da cewar bayan bindigogi ƙirar AK-47 da suka kama sun samu ma’adanin harsasai wato magazine guda tara da harsasai masu rai guda ɗari uku da takwas da kuma ƙananan albarusai masu tsawon mita 7.6 guda takwas.