Daga CMG HAUSA
A yayin taron ganawa da manema labarai game da aikin kandagarkin annobar COVID-19 da aka shirya yau Talata da safe, an bayyana cewa, a halin yanzu, an cimma nasarar kawar da ƙwayoyin cutar COVID-19 baki ɗaya a yankunan ƙananan hukumomi 16 dake birnin Shanghai na ƙasar Sin.
A jiya Litinin 16 ga wata, an tabbatar da sabbin mutane 77 da suka kamu da cutar, sannan wasu mutane 746 da suka kamu da cutar, amma ba tare da nuna alamun cutar ba a birnin Shanghai. Kuma, dukkansu suna zaune ne a cikin yankunan da aka kilace.
Bugu da ƙari, bisa nazarin da masana suka yi, za a dawo da harkokin yau da kullum a duk fadin birnin yadda ya kamata bisa matakai guda uku. Kuma, bisa shirin da aka tsara, daga ranar 1 ga watan Yuni zuwa tsakiyar watan Yuni, za a ci gaba da aiwatar da tsaurarrun matakan kandagarkin cutar bisa ƙa’idar rigakafin yaɗuwar cutar, da tafiyar da harkokin kasuwanci da aikin kandagarkin annoba yadda ya kamata.
Mai Fassarawa: Maryam Yang
