Wa zai yarda Amurka ta goyi bayan yankin Taiwan don halartar babban taron lafiya na duniya?

Daga CMG HAUSA

A gabannin babban taron ƙasa da ƙasa kan harkokin kiwon lafiya karo na 75, wasu ‘yan siyasar Amurka sun sake ƙulla makirci, na nunawa yankin Taiwan goyon baya don halartar taron.

Kwanan nan ne, shugaban Amurka ya sa hannu kan wani shirin doka, inda ya buƙaci sakataren harkokin wajen ƙasar, da ya taimaki yankin Taiwan, don sake dawo da matsayinsa na dan kallo a hukumar WHO, ta yadda zai samu damar halartar taron. Irin wannan abu, shisshigi ne da aka yi cikin harkokin cikin gidan ƙasar Sin, wanda kuma ya sabawa babbar manufar kasancewar ƙasar Sin ɗaya tak a duniya, da ƙa’idojin wasu sanarwar haɗin-gwiwa uku da aka daddale tsakanin Sin da Amurka.

Baya ga wasu ‘yan ƙasashe ƙalilan da suka kulla hulɗar diflomasiyya tare da Taiwan, gami wasu ƙasashen yammacin duniya kaɗan, babu wata ƙasa da ta goyi bayan Amurka.

Batun da ya shafi yankin Taiwan, batu ne mafi muhimmanci a dangantakar Sin da Amurka, wanda ya shafi babban muradun ƙasar Sin. Ya dace ƙasar Amurka ta cika alƙawarin siyasar da ta daukawa ƙasar Sin, ta dakatar da kawo illa ga babbar manufar kasancewar ƙasar Sin daya tilo a duniya, don tabbatar da matsayar da shugabannin ƙasashen biyu suka cimma tare. Yin fuska biyu kan batun Taiwan da Amurka ta yi, zai ƙara kawo illa ga kwarjininta a fannin siyasa.

Fassarawa: Murtala Zhang

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *