Daga AMINA YUSUF ALI
A ranar Litinin ne dai Sarkin Illori Alhaji Ibrahim Sulu-Gambari, ya bayyana mubaya’arsa ga ɗan takarar shugabancin Nijeriya a APC, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu.
Basaraken ya bayyana haka ne yayin amsar baƙuncin mambobin ƙungiyar yaƙin neman zaɓen Tinubu mai suna, South West Agenda for Asiwaju 2023 a fadarsa dake Ilorin. Inda ya bayyana cewa: “Tinubu ya cancanci zama shugaban ƙasar Nijeriya na gaba”.
Amma abinda ya fi ɗaukar hankali ga wannan mubaya’a da basaraken ya yi ga Tinubu shi ne mubaya’ar ta zo ne a dai-dai lokacin da ɗan asalin jiharsa kuma Mariƙin ɗaya daga cikin sarautun gargajiya a masarautar Illori, tsohon Shugaban Majalisar dattijai, Sanata Bukola Saraki shi ma yake neman takarar wannan kujerar.
A cewar Gambari, Tinubu ya kawo cigaba a ƙasar nan sosai, sannan ya kawo cigaba a rayuwa al’ummar Nijeriya sosai.
Daga nan Sulu-Gambari ya shirya wa Tinubu wani ƙwarya-ƙwaryar taron addu’a sannan kuma ya yi alƙawarin zai cigaba da yi masa addu’a a fili da ɓoye don gani ya samu nasara.
Da ma dai tun da fari Shugaban ƙungiyar South West Agenda for Asiwaju 2023 na ƙasa, Sanata Dayo Adeyeye ya bayyana wa sarkin cewa, Sun zo fadarsa ne don neman tubarrakin ƙaddamar da kamfe ɗin takarar Tinubu don zama shugaban ƙasar Nijeriya a zaɓen mai zuwa. Ya ƙara da cewa, ƙungiyar tasu ta kai makamanciyar wannan ziyara ga sarakunan gargajiya guda 300 a faɗin ƙasar nan.
Sanata Adeyeye ya ƙara da cewa, Tinubu shi ne mutumin da aza harsashi mai ƙarko don cigaban jihar Legas tare da samar da ƙashin bayan tattalin arzikinta. Don haka a cewar sa, mutum irin wannan shi ne ya cancanci ya zama shugaban Nijeriya a zaɓen mai zuwa.
