Ku manta baya mu haɗa kai – Gidan Dabino ga ’yan Kannywood

Spread the love

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano

Sabon shugaban haɗaɗɗiyar ƙungiyar masu shirya finafinai ta Nijeriya (MOPPAN) reshen Jihar Kano, Alhaji Ado Ahmad Gidan Dabino (MON), ya ce, duk da rigingimu da Kannywood ta ke ciki zai yi iya yinsa ya ga ya ɗinke duk wata ɓaraka a matsayinsa na shugaba.

Ya ce, “Wannan masana’anta da muka gina ta tun da jajayen sawunmu (mu na matasa) yau sama da shekaru 25, ya zama wajibi a gare mu da sauran ‘yan uwa da muke ta faɗi-tashi don ganin kada wannan masana’anta ta wargaje, mu haɗa hannu don mu daɗa samar mata da inganci da nagarta a idanun duniya. Dukkaninmu mun san irin ƙalubalen da wannan masana’anta take ciki da rigingimu da tashin-tashina da harbatta mati da ake ta samu a cikin da’irar Kannywood.”

Ta cikin wata takarda da aka raba wa manema labarai a ranar Larabar makon jiya a Birnin Kano, Shugaban na Moppan a Kano ya ce, “Mun shiga wannan shugabanci ne da burimu na farfaɗo da mutunci da ƙima da darajar da wannan masana’anta take da ita.

“Da yawanmu mun san dalilin gina wannan masana’anta shi ne, ilimintarwa, faɗakarwa da kuma nishaɗantar da al’ummarmu cikin hikima ta wasan kwaikwayo, wanda muka gada daga iyayenmu, mutane irin su; Marigayin Kasimu Yero da Danjuma Katsina da Daudu Ahmad Galadanci da Mustapha Muhammad Danhaki da Mansur Kwalli da Haruna Danjuma da Bawa Garba na cikin shirin Baban Larai da Abdu Kano (Karkuzu) da sauransu. Don haka fatanmu shine, mu dawo da ƙima da martabar da ake yi wa masu sana’ar fim a da ko ma fiye da da ɗin, waɗanda suke tallata kyawawan al’adun Bahaushe, Fulani da Barebari da dukkan ƙabilu da suke wannan yanki na arewacin Nijeriya da ma ƙasa bakiɗaya. Hakan ba zai yiwu ba, sai da haɗin kan ku da za mu shugabanta da kuma uwar ƙungiya MOPPAN ta ƙasa, in ba ku ba da haɗin kai ba, zai yi wuya ƙwarai da gaske hakan ta samu. Mun lura cewa muna buƙatar ilimin wannan sana’a tun daga ƙirƙirar labari har zuwa kasuwancin fim ɗin.”

Ya ƙara da cewa, “Finafinan Hausa na Kannywood sun fi duk wata kasuwar shirya finafinai a Afrika, domin akwai mutane masu sha’awar kallon finafinanmu sama da miliyan 300 a Afrika ta Yamma da ta Arewa da ta Gabas da kuma Afrika ta Tsakiya. Ban da sama da miliyan 100 da suke buƙatar finafina Hausa a Gabas ta tsakiya da ƙasashen Turai da kuma Amurka ta Arewa, wato USA da Canada.

“Idan aka yi tsari mai kyau, muna tabbatar muku fim ɗin Hausa ya fi kowanne irin kasuwanci da kuke tunanin za ku yi a matsayinku na fasihai, saboda haka idan muka ci gaba da wasa da sakaci da riƙon sakainar kashi, idan muka gyara, irinsu Dangote, Abdulsamad da A.A. Rano da kuma ƙannensu suka fahimci sana’ar fim sana’a ce da take samar da maƙudan kuɗaɗe a duniya, za su shigo ne da ƙarfin su kamar yadda suke yin sauran kasuwancinsu.

“Wannan shi ya sa za mu tsaya tsayin daka wajen horar da ‘ya’yan wannan masana’anta yadda za su ci amfanin wannan masana’anta tun kafin manyan masu kuɗi su yi wuf da ita. Don haka muke neman ku manta komai da ya faru a baya, na sa’in sa da cacar baki ku zo mu haɗa karfi da ƙarfe don mu samar da ingantattun shirye-shirye da za su iya shiga kowacce nahiya ta duniya, ta yadda kowa zai iya cin albarkar wannan sana’a ta fim.”

Taron dai ya samu halartar manya manyan ‘yan wasa da suka haɗa da; Umar Gombe da Alasan kwalli da Sunusi Shehu Daneji da Ibrahim Mandawari mai unguwar Mandawari da Hamisu Lamido Iyantama da Ladidi Fagge da Aminu Abubakar (ALA) Maryam CTV da sauransu da dama.

By Editor