Sanarwar ministocin ƙungiyar G7 ta keta ƙa’idar ƙasa da ƙasa ce dake neman rura wutar rikici

Daga FAEZA MUSTAPHA

A baya-bayan nan ne, ministocin harkokin wajen ƙasashen ƙungiyar G7 suka fitar da wata sanarwa bayan taron da suka yi, inda a cikinta suka bayyana wasu buƙatu ga ƙasar Sin, waɗanda suka yi su bisa son zuciya da zarge-zarge marasa tushe, da gazawa wajen mutunta cikakken ’yancin kan ƙasar.

Cikin sanarwar, sun ce sun damu da yanayin kwanciyar hankali a tsibirin Taiwan. Amma sam ƙasashen yamma ba su damu da hakan kamar yadda suke furtawa ba. Sanin kansu ne cewa, zaman lafiyar yankin ya dogara ne da janyewarsu daga yi wa harkokin gidan Sin katsalandan da kuma mutunta manufar ƙasar Sin daya tak a duniya da ƙaurace wa bi ta bayan fage wajen ƙulla wata alaka da yankin, wanda mallaki ne na ƙasar Sin, da kuma daina ingiza wasu tsiraru wajen rajin neman ɓallewa.

Har ila yau, sun tabo batun Xinjiang da Tibet, suna masu cewa a kare haƙƙoƙin bil adama a yankunan. Haƙiƙa ƙasashen yammacin duniya su kan manta cewa, gwamnatin da tsarin demokraɗiyyar kasar Sin, su kan sanya al’umma ne a gaban komai. Ƙasar Sin ba ta maraba da duk wani abu da zai taba walwalar al’ummarta. Kana mai daki shi ya fi kowa sanin idan yake yoyo, wato mutanen waɗannan yankunan ne ke da alhakin ƙorafi ba wasu daga waje ba. Ƙasar ta sha nanata cewa tana maraba da ƙasashen nan su ziyarci yankunan don gane wa idonsu yanayin da suke ciki, amma maimakon hakan, sai suke zama suna kitsa karairayi da zummar shafa mata baƙin fenti.

Bugu da ƙari, sun tabo batun Hong Hong da kare haƙƙin bil adama da demokraɗiyya a yankin. Idan ba a manta ba, irin waɗannan furuci ne suka haifar da tashe-tashen hankula a yankin na Hong Kong a shekarun baya, wannan alama ce ƙarara dake nuna cewa, ba ƙaunar mutanen Hong Kong din da zaman lafiyarsa suke ba. Idan da sun damu, da ba za su taba ingiza bata gari wajen tayar da hankalin jama’a ba, lamarin da ya haifar da asarar dukiyoyi da tattalin arzikin yankin.

Ba sai an fada ba, irin waɗannan kalamai da ƙasashen yammacin duniya suke kan ƙasashen da suke ganinsu a matsayin barazana da suka zabi neman hanyar raya ƙasa da ta dace da yanayinsu, bai taba haifar da wani da mai ido ba, illa ƙara rura wutar rikici da kawo tsaiko ga ƙoƙarin da ake na wanzar da zaman lafiya da haifar da yaƙe-yaƙe.