Matasa a siyasa

Daga MARYAM BATOOL

Ita dai siyasa tana nufin haɗa yarjejeniya tsakanin mutane, domin su zauna tare duk da mabambantan ra’ayoyinsu, ƙabilu da addinai a birane da ƙasashe.

A manyan ƙasashe mutane da dama kan dauki dogon lokaci wajen tsayar da yarjejeniyar siyasa.

Waɗannan mutane su ake kira da ‘yan siyasa. ‘Yan siyasa da kuma ragowar Al’umma sukan haɗu don samar da gwamnati da tafiyar da ita.

Kafin kafuwar sabuwar gwamnati akwai wasu ƙa’idoji da ake bi domin samun tsayayyun shugabanni nagari. Al’umma ƙasa da garuruwa sukan haɗu gabaɗaya domin zabar wanda suke so bayan jam’iyoyi sun fitar da ‘yan takarar su ta hanyar zaɓen cikin gida.

Akan yi kamfen domin jan ra’ayoyin Al’umma sannan kuma su bayyana kyakyawar niyyarsu ga Al’umma.

Matasa masu ra’ayij siyasa a wannan lokacin suma sukan fito takara kuma su shiga gwagwarmayar samun shiga, amma sananniyace cewa wannan gwamnatin ta mu ba ta cika bawa matasa dama ba har su zama su ma ana gogawa da su a fannin siyasa da kuma mulki. Duk kuwa da ƙoƙarin da wasu manyan suke yi da ma su matasan kan su. Akan samu matsaloli daban-daban tun daga kan jam’iyoyi da tsadar form din takara da kuma ragowar wasu tsarrabe-tsarrabe da yake sa masu sha’awar takarar su haƙura ba don suna so ba.

Sannan a wani ɓangare daban akwai wasu matasan da ake amfani da su domin yaɗa manufar siyasa da kuma kamfen. Wasu lokutan babu wani abu da za a biya su amma wahala iri-iri babu kalar wacce ba sa yi domin ganin samun nasarar ubangidan su. Duk da kallon da ake musu na marasa aikin yi kuma marasa amfani a cikin al’umma akan je a neme su kuma a amfana da su. Da yake da yawan mu matasan babu wani abu da muke yi sai ya zama mun yi na’am kuma mun karbi tayin hannu biyu ba tare da mun yi dogon tunani kuma mun tantance ra’ayoyin mu ba.

A cikin irin wannan ɗauki ba dadi ne da ake yi wa matasa akan samu wasu daga ciki wanda su dama suna da wata ɗabi’ar ta su da za ta taimaki ko kuma za ta zama ado ga ‘yan siyasar, wanda mafi yawancin su kuma wanda aka fi gani sune‘yan shaye-shaye da suke harkar dabanci.

Shi dai shaye-shaye yana nufin amfani da wani abu da zai gusarwa da mutum hankali ko ya saka maye ta hanyar sha, ci, shinshinawa ko busawa ko kuma allura.

Rabi da kwatan matasa a bincike ya nuna suna shaye-shaye, abun ya zama ado a wasu ɓangarori da idan ma har baka yi ana yi maka wani kallo na rashin wayewa. Duk da yadda iyaye, malamai,marubuta. dattijai da masu faɗa a ji sukan yi ƙoƙarin su wajen nusar da al’umma gabaɗaya hatsarin da yake a tare da shi amma abun ƙara ƙaruwa yake. Abubuwan da yawa sukan sa mutum ya fara shaye-shaye daga cikin su akwai rashin kulawa da ake nunawa matasan a lokacin da suka fi buƙatarta, nisantasu da abubuwan da suke ba su kariya da kuma abubuwan da suke so wanda yake haddasa musu damuwa, inda sukan je su nemi hanyar sa za ta gusar musu da wannan damuwar kuma har su faɗa shaye-shaye.

Akwai kula abokanai da kawayen da ba na kirki ba wanda su dama suna shaye-shayen ko kuma suna da niyyar yi, amfani da magani ba tare da izinin likita ba, sai ya zama da an ɗan ji wani abu ko kuma an fara rashin lafiya maimakon a je a ga likita ya bada magani sai aje kemis a siya a fara sha wanda hakan ba dai-dai bane domin kuwa ko da ka san irin kalar maganin da kake buƙata bai zama lallai an san irin adadin da ake buƙata ba.

Akwai wanda su kuma suna son su ji me ake ji ne a shaye-shayen, wasu kuma don sun ga wani wanda yake burge su musamman mawaƙa da ‘yan fim, suna yi shiyasa su ma sai su faɗa, da dai sauransu.