Maza masu duka da wulaƙanta matansu sam ba su da laifi!

Daga AMINA YUSUF ALI

Barkan mu da sake haɗuwa a wani makon a filinmu mai albarka, Zamantakewa na jaridarku mai farin jini ta Blueprint Manhaja. 

Da farko dai shi duka a zaman aure da maza suke yi wa mata abu ne a al’adance da ddinance ma bai kamata ba, kuma abu ne da yake ci wa mata tuwo a ƙwarya. Duk da dai shi duka a gidan aure ba Hausawa suka fi yinsa ba. Wasu ƙabilun na Nijeriya sun fi yinsa. Sai dai shi ma Bahaushe yana nema ya ara ya yafa.  Abin tambaya, me yake jawo duka a zaman aure?

Babban abinda yake jawo duka a zaman aure ba ya wuce zafin zuciya daga ɓangaren namiji. Yayin da matarsa ta yi masa laifi, zuciya ta kufulo shi ya zuciya ya hau dukan ta. Wani laifin ma da maza suke dukan mace bai kai ya kawo ba. Kuma daga sanda ya tsaga ya ga jini, ma’ana idan ya yi ya ci riba, shikenan ya ga waje. Kullum ana laifi kaɗan, sai ya ce, duka.

Wani lokacin ma ba ita za ta kar zomon ba, wani ne kawai zai ɓata masa rai a can waje, amma sai ya zo gida ya nemi dalili komai ƙanƙantarsa ya rufe ta da duka don ya huce wancan haushi da aka ba shi. Wani kuma shaye-shaye ne yake kai shi ga dukan mata. Kuma ma fi yawan lokuta zai iya ji mata rauni, wani lokacin ma idan da ƙarar kwana, ta rasa ranta. 

Sai dai kuma a ganina mazan da suke aikata wannan ta’addar ta dukan mata, anya suna da laifi?

Ni dai har ga Allah ban fiye ganin laifinsu fiye da na matan ko na al’ummar gari ko iyaye da dangin matar da nasa ba. Xanadam yana da wata ɗabi’a ta cigaba da yin abinda yake ko da kuwa mara kyau ne, in dai har zai samu goyon bayan wasu mutane. Ko kuma zai samu wata hujja ya dogara da ita.  A ganina, namiji madokin mata ba zai taɓa samun yin haka ba sai da ƙwarin gwiwa da taimako daga wasu mutane ko wasu abubuwa. 

Da farko ma dai ina mamakin mace ki zauna dafi’an har namiji ya jibge ki, ba ki taɓuka komai ba. Daga kin ga ya zuciya ba za ki gudu ki bar wurin ba? Ƙarfinku ma ba ɗaya ba. Idan kika zauna idan da ƙarar kwana ma halaka ki zai yi. Sannan ya miki duka na ɗaya, ya yi na biyu, wataƙila ma da na uku.

Ke ko baiwar Allah zaman me kike yi a gidan? Na san za ki ce zaman ‘ya’yanki. To amma idan kika bari ya kashe ki ba kya Duniya, wa zai kula da yaran da kika bari? Sai ki yi tunani ki yi karatun ta-nutsu. Kuma idan tarbiyyar yara kike gudu kada ta lalace idan kin bar gidan, shi ya sa kika nace sai kin zauna, to wacce tarbiyya za su koya a wajen ganin ubansu yana dukan uwarsu kullum? Ko kuma wanne mutunci za ki yi a idon ‘ya’yan ke da ubansu bayan kullum suna ganin yana jibgar ki?

Ƙarshe dai su girma su fara harzuƙa da ganin ubansu yana dukan ki zuciya ba ƙashi, sai su kasa daurewa su shigar miki ko su zage shi, ko su rama miki dukanki. Kin ga karshe dai ya vata muku tarbiyyar ‘ya’ya kuma yana neman haɗa su da fushin Ubangiji. Ke kuma a lokacin ba abinda kike buƙata illa yaran su zama masu albarka su tallafe ki, sai ga shi sun ɓuge da neman fushin Allah wanda zai iya sa rayuwarsu cikin gararin da bala’i. To kinga duk yadda kuka juya, zaman ba shi da wata rana ko alfanu a rayuwarku da ta yaranku. Gara ki arce tun kina da damar yin haka.

Kada ku saurari masu cewa, ki yi haƙuri ki zauna zai gyara. To yaushe zai gyara ɗin? Da wuya madokin mata ya daina fa in dai ba wani ikon Allah ba. 

To dalilin na biyu da nake ganin madoka mata ba su da laifi shi ne, ba mu mai da shi abin ƙyama a tsakanin al’umarmu ba. Misali, idan mutum yana dukan matarsa kuma kowa ya san hakan mutane sukan cigaba da mu’amala da shi ba tare da wariya gare shi ba. Za a gaisa da shi, wani ma ya ja Sallah a bi shi, a ci abinci da shi ba tare da an yi la’akari da cewa ya tashi daga sahun mutane ya shiga na dabbobi ba. Abin takaicin ma, idan ya sake neman wani auren za a iya ba shi dai a cikin wannan al’umma da yake rayuwa.

Musamman idan ya samu ɗiyar marasa galihu, balle a ce yana da abin hannunsa. Ai talakawan unguwa rububin aura masa yaransu suke yi don kwaɗayin abin Duniya. Sai an yi auren matsaloli sun taso a zo a yi ta maganganu, daga qarshe ya sako ta, kuma a sake ba shi wata ya aura! Kuma dukan dai ba zai fasa ba duk wacce ya aura. Sannan kuma ba za a samu wani ko wasu da za su yi masa nasiha ba. To meye laifinsa a nan? Wa zai ga wannan garavasa ya ƙyale? Idan an hana shi matar aure ina zai samu wacce zai aura ya yi wa duka? 

Sannan dalilina na uku shi ne, iyayen matar su suke ba wa maza goyon baya ya doke ta. Da farko ma dai an aurar da ita ga namijin da ba a yi cikakken bincike a kan rayuwarsa da mu’amalarsa ba. Ko an yi bincike an gano yana duka, iyayen su ƙaryata. Idan yana da kuɗinma su ce ana musu baƙin ciki ‘yarsu za ta huta. Idan kuma a unguwarsu ma yake, kuma kowa ya san halinsa, sai ka ga suna alaƙarta laifin da mata ko matansa da yake duka. Suna aibata su, suna nuna laifinsu ne ya sa ake dukan. Amma abinda yarinya da iyayenta suka manta shi ne, bulalar da ta doki uwargida, tana nan tana jiran amarya. Ita ma sai ya dake ta yadda ya daki sauran ko ma fiye da haka. Sai a yi hattara makwaɗaita. 

Sannan abu na huɗu, rashin faɗa masa gaskiya daga dangi zuwa iyaye. Sai ka namiji madokin mata ne, amma kaf danginsa musamman idan yana da hali ba wanda zai tsawatar masa ko ya yi masa nasiha ya daina. Sai ma ka ji suna goyon bayansa a kan matansa ne ba su da hali. Ya ilahi, duk matan Duniya ba su da hali sai shi, madokin mata? Wannan tsabar don zuciya ne. Su kansu ba za su so a yi wa ‘ya’yansu mata ba. Me ya sa kuma kake goyon bayan a yi wa ɗiyar wani? Wallahi da wani zai taimaka ko da da nasiha ne a samu ya daina, zai sami ɗimbin lada. Bugu da ƙari kuma kun ceto ɗanuwanku daga uƙubar Ubangiji. Domin zaluntar mata ta hanyar duka ba koyarwar musulunci ba ce, kuma Allah ba zai bari ba.

Kuma sannan kada mu manta, akwai illoli da yawa tattare da dukan mace kamar, yi mata Lahani ko kisa, ɓata tarbiyyar yaran da kuka haifa, zubar da mutuncinka da nata a makwabta da iyayenta da sauran dangi, yaranta za su ƙullace ka kuma ba za su ta a ɗinka ba, sannan wata rana ma su rama ko su tsawatar maka. 

Da a ce al’ummarmu za ta gane, da ta ware masu wannan ɗabi’a wajen girmamawa, ko ba da wani shugabanci, ko zaɓensu a siyasa ko kuma a ba su auren ‘ya’yansu. Yin shiru da rashin ɗaukar matakai a kan abinda suke aikatawa yana sa wa su dinga ganin kamar Duniya ta ba su goyon bayan cigaba aiwatar da wannan mummunar ɗabi’ar tasu. 

Sannan iyaye su daina tilasta wa yaransu mata da su koma su cigaba da zama da maza masu dukan mata. Domin shi aure ba dole a cikinsa idan da cutarwa musulunci ya yarda a raba. Gara ku karɓe ta a bazawara a kan matacciya. Domin dukan na iya halakar da ita. 

Kai kuma madokin mata ka sani, Lusari ne kai wanda ba ya bin sunnar Annabi (SAW). Kuma dukan iyali yana rusa gida. Iyalinka su daina ganin mutuncinka. Watarana ma yaranka za su iya ƙalubalantar ka. Sannan yaranka maza za su ɗauki wannan ɗabi’ar su cigaba da aikatawa ga nasu matan.

Kuma sannan ka sani, duka ko ga ‘yayanka bai kamata ba, balle ga matarka da ka aura da amana don kana son ta, tana son ka. Duk girman laifin da za ta yi maka ba zai wuce ka yi mata faɗa ko nasiha ba, ku zauna ku fahimci juna. Idan abu ya faskara, rabuwar aure fa halas ce. Sai a rabu ba tare da an ci mutuncin juna ba.  Da fatan Allah ya yi mana jagora. Babbar godiya ta musamman ga ƙanina Muhammad Ubale Ƙiru wanda rubutunsa shi ya ja hankalina ga wannan maudu’i. Da fatan Allah saka masa da alkhairi ya ƙara taimakonmu bakiɗaya.

Mu haɗu a wani makon, idan Allah ya kai mu.