An kammala baje kolin cinikayyar zamani na duniya na farko a Hangzhou

Daga CMG HAUSA

A yau ne, aka yi nasarar kammala bikin baje kolin cinikayya na zamani na duniya karo na farko, a birnin Hangzhou na kasar Sin, inda aka samu halartar manyan kamfanoni na cikin gida da ketare sama da 800, tare da yin cinikiyyar da ta kai yuan biliyan 37.4.

Baya ga mayar da hankali kan manyan fannoni uku na “Internet Plus”, sabbin kayayyaki da kiwon lafiya, bikin baje kolin kayayyakin fasahar zamani na bana, ya kuma sanya hannu kan ayyukan 89 tare da manyan kamfanonin kasa da kasa, da zuba jari na kusan yuan biliyan 110.

Mai fassarawa: Ibrahim daga CMG Hausa